An Tsaka Da Karancin Naira, An Kama Wani Da Tsabar Sabbin Kudi N250,000 Na Bogi

An Tsaka Da Karancin Naira, An Kama Wani Da Tsabar Sabbin Kudi N250,000 Na Bogi

  • A yayin da ake fama da karancin takardun naira a Najeriya, an kama wani Celestine da sabbin kudi na bogi fiye da N250,000 a Ekiti
  • Wanda ake zargin bayan ya shigo hannu ya fada wa jami'an Amotekun cewa wani ya bashi kudin ba tare da ya san cewa na bogi bane
  • Kwamandan Amotekun na jihar Ekiti, Birgediya Janar Joe Komolafe (mai murabus) ya gargadi mutane su yi takatsantsan da bata gari da ke fakewa da karancin nairan don yaudara

Jihar Ekiti - Jami'an Amotekun a jihar Ekiti sun cafke wani mutum mai suna Celestine, da kudin bogi na sabbin takardun N1000 da suka kai N250,000, rahoton The Punch.

Celestine wanda ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa haifafan Anambra amma mazaunin Legas, kuma yana hanyarsa ne daga Legas zuwa Isanlu a jihar Kogi don siyan goro da namijin koro aka kama shi da kudin na bogi.

Kara karanta wannan

Ke duniya: An kama matashi bayan yiwa mahaifinsa barazanar kisa a wata jihar Arewa

Wanda ake zargi
An Tsaka Da Karancin Naira, An Kama Wani Da Tsabar Sabbin Kudi N250,000 Na Bogi. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Ban san na bogi bane, wani ya bani kudin na bogi, wanda ake zargi

Wanda ake zargin wanda ya yi magana a hedkwatar Amoketun da ke Ado Ekiti, inda aka yi holensa tare da kudin ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fada cikin yanayi ba da saninsa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wanda ake zargin ya ce:

"Na karbi sabbin nairan ne daga hannun wani kwastoma a jihar Legas ba tare da sanin cewa jabu ne ba.
"Bayan an kama ni, na yi kokarin in tuntube shi don a sako ni, har yanzu ina jira in ji daga gare shi."

Kwamandan Amoketun na jihar, Birgediya Janar Joe Komolafe (mai murabus) ya ce jami'an hukumar sun kama wanda ake zargin ne a Omuo Ekiti a karamar hukumar Ekiti East na jihar Ekiti bayan ya kashe takardun N1000 na bogi a kasuwa.

Kara karanta wannan

Ka Kadde: Bidiyon Yadda Aka Kama Wani Mutum Dauke Da Sabbin 'Yan N500 Na Bogi, Jama'a Sun Girgiza

Komolafe ya ce:

"Jami'an Amotekun sun sanar da wasu masu sana'ar POS cewa an gano takardun nairan na bogi a yankin. Bayan samun sanarwar, mutanen mu sun bazama sun fara aiki sun kamo wanda ake zargin da kudin bogi mai yawa.
"Mutanen mu sun samu sahihan bayani cewa wanda ake zargin ya shio garin da misalin N250,000 na sabbin N1000. Yanzu ana masa tambayoyi a ofishin mu. Za a mika shi hannun yan sanda don zurfafa bincike da hukunta shi bayan mun kammala bincike."

Kwamandan na Amotekun din ya kuma gargadi mutanen gari cewa:

"Ku yi takatsantsan da wasu bata gari wanda ke son yin amfani da damar karancin takardun naira a kasar su rika damfarar mutane."

A wani rahoton a baya kun ji cewa dan jarida a Najeriya mai suna Ali Ahmed Geidam ya bayyana yadda wani mai sana'ar POS ya bashi sabbin naira na jabu.

Hakan yasa ya ankarar da yan Najeriya su rika takatsantsan da irin kudaden da ake basu.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

Asali: Legit.ng

Online view pixel