Ku Daure Ku Karbi Tsoffin Takardun Naira, Gwamna Obaseki Na Edo Ya Roki Al’ummar Jiharsa

Ku Daure Ku Karbi Tsoffin Takardun Naira, Gwamna Obaseki Na Edo Ya Roki Al’ummar Jiharsa

  • Gwamnan jihar Edo ya bayyana bukatar al’ummar jiharsa da su ci gaba da kashe tsoffin takardun Naira bayan umarnin kotun koli
  • Gwamnatocin jihohi sama da 10 ne suka maka gwamnatin tarayya da CBN a kotu kan batun sake fasalin Naira da tsawaita wa’adin kashe tsoffin kudi
  • Ya zuwa yanzu, wasu kasuwanni da shagunan siyayya ba sa karbar tsoffin kudaden a bangarori daban-daban na Najeriya

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya roki al’ummar jiharsa da su yi hakuri suke ta’ammuli da tsoffin takardun Naira na N500 da N1000 bayan umarnin kotun koli har zuwa 31 ga watan Disamba, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin jihar Edo na daga cikin gwamnatocin jihohi da suka hada kai tare da maka gwamnatin tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) a kotu don neman tsawaita wa’adin kashe tsoffin Naira a kasar nan.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Yadda Gwamnan CBN Zai Jefa Kan Shi a Cikin Matsala – Shugaban PACAC

Idan baku manta ba, kotun kolin ya rushe tare da yin watsi da wa’adin da CBN ya bayar na 10 ga watan Faburairu kan cewa a daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000.

Gwamna ya ce ya kamata mutane su ke karbar tsoffin kudi
Sabbin Naira da aka buga na ci gaba da jan hankali a Najeriya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Gwamna ya roki ‘yan jiharsa

A nasa bangaren, bayan hukuncin kotun koli gwamna Obaseki ya fitar da wata sanarwa ta hannun Chris Nehikhare, kwashinansa na yada labarai, inda yace ya kamata mazauna jiharsa su gwama amfani da tsoffi da sabbin Naira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wani yanki na sanarwar kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito:

“Tare da hukuncin kotun koli, an hutar da jama’a daga cece-kuce kan yawon kudade kuma ana kira ga jama;a da su karbu kudin kuma su kasuwancinsu dasu.
“Muna kara gano hanyoyin harkalla da kudi irinsu tiransfa, da dai sauransu, yayin da dukkan wasu batutuwa na wadatuwar tsabar kudi aka warware su daga bangarorin gwamnati da suka dace.”

Kara karanta wannan

Naira: Gwamnan APC Ya Fusata, Ya Faɗi Babban Laifin Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin N500 da N1000

Har yanzu ba a karbar tsoffin kudi a wasu bangarorin Najeriya

A wani labarin, kunji yadda rahoto ya bayyana halin da al’umma ke ciki a wasu jihohin kasar nan bayan hukuncin kotun koli cewa a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira.

A binciken da aka yi, manyan shagunan siyayya, gidajen mai da tashoshin motoci da yawa ba sa karbar tsoffin kudaden.

A zantawan da aka yi da jama’a, sun ce ba sa karbar kudin ne saboda gudun yin asara, duk da kuwa bankuna na ba mutane tsoffin takardun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel