Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili

Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili

  • Jam'iyyar Labour ta koka cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, tana kokarin kawo mata cikas a yunkurinta na kwato nasararta a kotu
  • Dr Yununsa Tanko, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Labour ya yi wannan zargin
  • Tanko ya gargadi hukumar INEC cewa idan ba ta bi umurnin da kotu ta bada ba na bawa Peter Obi da LP damar bincika kayayyakin da aka yi zabe da su, za su tura magoya bayansu su mamaye ofisoshin INEC

Jihar Legas - Jam'iyyar Labour ta zargi hukuman zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, da kawo cikas ga karar da ta shigar na kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, Daily Trust ta rahoto.

A wurin taron manema labarai a Legas, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar, Dr Yunusa Tanko, ya zargi INEC da saba umurnin kotun sauraron karar zaben shugaban kasa wacce ta bai wa jam'iyyar da dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi, daman duba ainihin kayayyakin da aka yi amfani da su yayin zaben.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Tabbatarwa 'Obidients' Cewa Zai Kwato Musu Nasararsu, Bidiyo Ya Fito

Magoya Bayan LP
Jam'iyyar Labour ta yi barazanar yin zanga-zanga a ofishin INEC. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce an gabatarwa INEC takardar kotu a ranar 3 ga watan Maris duk da cewa hukumar ta samu wakilci a zaman kotun lokacin da aka bada umurnin.

Ya ce jam'iyyar ta kuma aika wasika ga hukumar zaben a ranar 6 ga watan Maris, tana tunatar da ita cewa ba ta riga ta bi umurnin kotun ba.

Yunusa ya yi barazanar cewa jam'iyyar Labour za ta umurci magoya bayanta su yi zanga-zangan lumana a dukkan ofisoshin INEC kan rashin bin umurnin kotun, yana mai cewa dole ne kowa ya bi umurnin kotu a karkashin dimokradiyya.

Wani sashi na kalamansa:

"Muna kira ga al'umma su lura da rashin bin umurnin kotu da hukuma irin INEC ke yi, kuma wani mataki ne da gangan don kawo cikas ga jam'iyyar Labour da dan takararta na shugaban kasa Peter Obi don samun daman gabatar da hujojinsu gaban kotu kan lokaci.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta ba Tinubu damar yin kwafin takardun da INEC ta yi aiki dasu a zaben shugaban kasa

"Don haka muna son mu bayyana cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wurin kira ga magoya bayan mu su yi tattaki zuwa ofisohin INEC a dukkan kasa a yanayi na lumana wacce doka ta halasta. An yi hakan ne domin a dakile rashin biyayya ga umarnin kotu da INEC ta yi."

Dr Tanko, wanda ya dage cewa Obi ne ya lashe zabe bisa sakamakon da wakilan jam'iyyarsu suka tattara daga akwatinan zabe, ya yi kira ga yan Najeriya su zabi yan takarsu a zabukan gwamna/yan majalisun jiha da za a yi ranar 18 ga watan Maris.

Wike ya bayyana mutumin da ya saka Peter Obi ya fita daga PDP

A wani rahoton, gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya magantu kan dalilin da yasa Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra ya fita daga PDP.

Wike ya ce jigon jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ne ya fada wa Obi cewa arewa za ta fitar da shugaban kasa na gaba.

Kara karanta wannan

Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel