Wani Mutum Ya Yaudari Kwararriyar Yar Gidan Magajiya Ya Tura Mata Alat Din N120,000 Na Bogi Bayan Gama 'Harka'

Wani Mutum Ya Yaudari Kwararriyar Yar Gidan Magajiya Ya Tura Mata Alat Din N120,000 Na Bogi Bayan Gama 'Harka'

  • An gurfanar da wani Samuel Oni a gaban kotun majistare da ke Ondo kan zarginsa da hadin baki da sata
  • Wata mata Blessing Olaitan, wacce ta kira kanta kwararriyar yar gidan magajiya ta ce Oni ya tura mata alat na bogi N120,000 bayan sun gama harka
  • Bayan wanda ake tuhumar ya musanta laifin, alkalin kotu ya bada belinsa kan N200,000, ya ce za a cigaba da shari'a ranar 17 ga watan Afrilu

Ondo - Hukumar tsaro na NSCDC reshen jihar Ondo, a ranar Alhamis, ta gurfanar da wani mutum, Samuel Oni, gaban kotun majistare a Akure, kan zargin damfarar yar gidan magajiya, Blessing Olaitan, kudi N120,000, rahoton The Punch.

Yayin zaman kotun, Olaitan ta fada wa kotu cewa ita kwararriyar yar gidan magajiya ne, ta kara da cewa bayan sun kammala harkarsu da mutumin, wanda aka yi karar ya karbi N80,000 daga hannunta da alkawarin zai mata tiransifa har da karin N15,000 kudin aikinta.

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

Gudumar kotu
Ana tuhumar wani da laifin hadin baki da sata bayan tura wa wata yar gidan magajiya alat din bogi. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma, daga bisani, ta gano cewa alat din bogi ne Oni wanda aka gurfanar a kotun kan tuhumar hadin baki da sata ya tura mata.

Tuhumar ta ce:

"Kai, Samuel Ono, da wasu a watan Maris na 2023, a Alagbaka, Akure, kun hada baki kun aikata laifi na satan kudi naira dari da ashirin na Mrs Blessing Olaitan, don haka sun aikata laifi da ya ci karo da sashi na 516 na dokar masu laifi Cap 37, Vol 1 na dokokin jihar Ondo na 2006."

Martanin wanda ake zargin

Bayan karanto masa tuhumar, Oni, ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da yi.

Lauyan wanda aka yi kara, Barista E.O. Nifemi, ya roki kotun ta bada belin wanda ya ke karewa, amma lauyan NSCDC, Mr David Ebriku, ya ki amincewa, yana rokon kotun ta tsare wanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: A rikicin shiga banki, mata ta gasawa dan sanda cizo, ya maka ta a kotu

Hukuncin alkalin kotu

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun Tope Aladejana, ya bada beli ga wanda ake tuhumar kan kudi N200,000 da mutum biyu da za su tsaya masa.

Ya kuma dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Afrilun 2023.

An kama saurayi da ke yaudarar yan mata ya sace musu waya da kudi bayan sun kwana a otel

A wani rahoton daban, kun ji cewa yan sandan Katsina sun damke wani dan shekara 31 kan zarginsa da amfani da shafukan sada zumunta yana kwanciya da mata yana musu sata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel