Garin Rikici Wajen Shiga Banki, Wata Mata Ta Gasawa Jami’in Dan Sanda Cizo, Ya Garzaya Kotu

Garin Rikici Wajen Shiga Banki, Wata Mata Ta Gasawa Jami’in Dan Sanda Cizo, Ya Garzaya Kotu

  • An gurfanar da wata mata a gaban kotu bisa zargin cin zarafin dan sandan da ke bakin aiki a jihar Ogun
  • A cewar majiya, lamarin ya faru ne a lokacin da rikici ya barke a layin shiga bankin Polaris a jihar
  • Wannan lamari ya dauki dumi, har an je gaban kotu, amma matar ta musanta zargin da ake yi mata

Jihar Ogun - An gurfanar da wata mata mai shekaru 43 a gaban kotu bisa zargin ta gasawa jami’in dan sanda cizo.

Rahoto ya bayyana cewa, zargin na nufin matar ta ci zarafin dan sandan da ke yiwa kasa aiki, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Hakazalika, an ce an gurfanar da ita ne a gaban kotun bisa zarginta da tada zaune tsaye da kuma farmakar jami’in dan sandan mai suna Insfekta Edoh Ogiri.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Karancin sabbin Naita ya sa mutane na samun matsala
Yadda karancin kudi ke hada mutane fada a Najeiya | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Yadda lamarin ya faru

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar rahoton kotu, dan sandan ya zo ne don shawo kan rikicin da ke faruwa tsakanin kwastomomin da ke bin layin banki a jihar Ogun.

Dan sanda mai gabatar da kara E.O Adaraloye, ya bayyana cewa, matar ta aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Maris da misalin karfe 1:30 na rana a bakin bankin Polaris da ke Otta

A cewarsa, laifukan da matar ta aikata ya zo daidai da tanadin sashe na 249 (d) da kuma 356 na kundin manyan laifuka na jihar Ogun, 2006.

Ta musanta zargin da ake mata

A bangare guda, matar da aka gurfanar din ta musanta zargin da ake tuhumarta dashi.

Mai shari’a Misis A.O. Adeyemi ta ba da belin marar a kan kudi N250,00, kana za ta gabatar mai tsaya mata a matsayin beli.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

A cewar mai shari’a, mai tsaya matan dole ya kasance mazaunin yankun kotu, kana za gabatar da shaidar yana biyan haraji ga gwamnatin jihar ta Ogun.

Daga nan ne kotun ya dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar 13 ga watan Maris din 2023 idan Allah ya kaimu.

Bankuna na ba da tsoffin kudi

A wani labarin kuma, kun ji yadda bankunan Najeriya ke ba da tsoffin kudi a ATM bayan da kotu ta yanke hukuncin ci gaba da kashe tsoffin Naira.

Sai dai, wasu bankuna sun ki cewa komai ko ci gaba da bayarwa da karbar tsoffin kudaden, inji rahotanni.

Ya zuwa yanzu, ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale kan karancin sabbin kudi, tsoffin ma na da wahalar samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel