"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

  • Babban kotu a jihar Kano na cigaba da sauraron karar dan kasar Sin da ake zargin ya kashe yar Najeriya
  • Dan Chinan ya bayyanawa kotu cewa bai yi niyyar kashe Ummita ba saboda har rauni ta ji masa
  • Alkalin kotu ya dage zaman zuwa karshen wata bayan kammala zaben gwamnoni a Najeriya

Kano - Dan kasar Sin, Mr. Frank Geng-Quangrong, ya gurfana gaban babban kotun jihar Kano ranar Alhamis, 9 ga Maris inda ya yi bayanin abinda ya faru ranar ake zargin ya kashe budurwarsa Ummita Sani.

Frank ya bayyana cewa bai yi niyyar kashe Ummita ba kuma ta ji masa rauni a marainansa, rahoton Vanguard.

Lauyan gwamnati, Mr. Muhammad Dan’azumi, ya gabatarwa kotu wayar hannu, sakonnin manhajar WhatsApp, hotuna da bidiyoyin maragayiyar.

Unnita
Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu
Asali: Twitter

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Kwankwaso Ya Karbi Bakuncin Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa

"Wadannan hujjoji sun hada da wayar wanda ake tuhuma, tattaunawar da sukayi a manhajar WhatsApp tsakaninsa da Ummukulsum daga ranar 13 ga Satumba zuwa 16, 2022."
"Saura sun hada da hotuna, rasidin zinari na milyan biyar da ya sayawa Ummukulsum da kuma 'Flash Drive' 4GB dauke da bidiyoyin margayiyar a cikin gidansa."

An kuna bidiyon a kotu inda aka ga marigayiyar tana wasa da wani kare mai suna Charlie, a gidan Frank dake Railway Quarters, Kano.

A bidiyo na biyu da aka bayyana a kotu, an ga marigayiyar a wani gida da take ginawa a Abuja tana zaune kan akwatunan kaya bakwai da Franka ya saya mata don aure.

Ta ji min rauni

Yayinda aka tambayarsa, Frank Dan China ya bayyanawa kotu cewa:

"Ita ta turo min bidiyon da kanta. Ban yi niyyar kashe Ummukulsun ba kuma ban son a kashe ni."
"Ta ji mini ciwo a maraina kuma ba zan iya nunawa kotu ba. Wannan ya sabawa al'adarmu da China kuma ni Musulmi ne."

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Antoni Janar na jihar Kano, Abdullahi-Lawan ya bayyanawa kotu cewa a ranar 16 ga Satumba, 2022, wanda ake tuhuma ya burmawa marigayiya Ummita wuka a gidansu dake Janbulo Quarters, Kano.

Frank dan China kuwa ya musanta wannan tuhuma da ake masa.

Alkali Sanusi Ado-Ma'aji bayan sauraron hujjojin ya dage zaman zuwa ranar 29 ga Maris domin cigaba da zaman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel