Canjin Kudi: Yadda Gwamnan CBN Zai Jefa Kan Shi a Cikin Matsala – Shugaban PACAC

Canjin Kudi: Yadda Gwamnan CBN Zai Jefa Kan Shi a Cikin Matsala – Shugaban PACAC

  • Idan Godwin Emefiele bai ba bankuna umarnin cigaba da kashe tsofaffin kudi ba, ya saba doka
  • Farfesa Itse Sagay SAN ya ce dole Gwamnan babban bankin kasar ya yi wa kotu biyayya
  • Shugaban kwamitin PACAC ya ce hukuncin da kotun koli ta zartar yana aiki a kan kowa a Najeriya

Lagos - Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele zai samu kan sa a cikin matsala idan dai bai yi wa kotun koli biyayya ba.

The Nation ta rahoto Farfesa Itse Sagay ya ce muddin Godwin Emefiele bai umarci bankuna su fara karbar tsofaffin N500 da N1000, zai saba doka.

A makon da ya gabata, kotun koli ta zartar da hukunci cewa tsofaffin takardun N500 da N1000 za su cigaba da aiki a matsayin kudi har Disamba.

Da yake jawabi a wani taro a Legas, fitaccen Farfesa, babban Lauya, masanin shari’a, Itse Sagay (SAN) ya ce wajibi ne a bi umarnin kotun koli.

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamna ya roki 'yan jiharsa, ya fadi abin da ya kamata su yi idan aka basu tsoffin Naira

Bayanin da Itse Sagay (SAN) ya yi

"Duk hukuncin da kotun koli ta zartar yana aiki a kan kowane mutum, har da gwamnati da ma’aikatunta da kuma Shugaban kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matsalar kurum ita ce babu abin da za a iya idan Shugaban kasa ya yi watsi da shi saboda yana da shamaki, amma dokar tana kan sa.
Gwamnan CBN
Gwamnan CBN a Ofis Hoto: guardian.ng
Asali: UGC
Babban banki bai bukatar jiran umarnin wani kafin ya yi biyayya ga hukuncin kotu domin yana cikin ma’aikatun gwamnatin tarayya.
Saboda haka idan CBN bai ba bankuna umarnin bin hukuncin ba, hakan yana nufin Godwin Emefiele yana yi wa kotun rashin kunya.

- Itse Sagay (SAN)

An rahoto Farfesan yana mai cewa ya ji labarin wasu bankuna sun fara karba da kuma bada tsofaffin kudin, ya ce su na sa rai a kara biyayya.

Farfesa Etannibi Alemika ya yi magana

Kara karanta wannan

Emefiele Ya Shiga Sabuwar Matsala Kan Rashin Umurtar Bankuna Su Rika Biya Da Karbar Tsaffin Kudi

A wajen taron da aka shirya domin jin ayyukan da kwamitin PACAC yake yi, Farfesa Etannibi Alemika ya ce akwai bukatar wayar da kan al’umma.

Masanin laifuffukan yana ganin zai yi kyau mutane su san kashe tsofaffin kudin ba laifi ba ne, kuma CBN ya fitar da jawabi mai bayanin wannan.

Dino Melaye ya soki canjin kudi

A wani rahoto da muka fitar, an ji tsohon Sanatan Kogi, Dino Melaye ya ce yaudarar jama’a aka yi da fito da sababbin N200, N500 da N1000 daf da zabe.

Kakakin kwamitin yakin zaben Atiku-Okowa a PDP ya ce an ba 'Dan takaran APC, Bola Tinubu sababbin Nairorin, yayin da su kuma aka hana su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel