Abubuwa 6 Da Tinubu Yake Buƙatar Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa

Abubuwa 6 Da Tinubu Yake Buƙatar Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa

  • NESG ta lissafa wasu abubuwa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya kamata ya tunkara da zarar an rantsar dashi
  • Ƙungiyar bada shawarar ta tattalin arziki tace, akwai buƙatar rage rashin aikin yi, bijiro da ababen more rayuwa da sauransu
  • Rahoton nata zayyano ƙalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta da kuma tasirin su ga kasar

Tun bayan gama zaɓen shugaban ƙasa tare da ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen ake ta samun shawarwari daga kwararru wajen inganta Najeriya.

Hakan ce tasa "The Nigerian Economic Summit Group (NESG)" ta fitar da wani dunƙulin shawarwari guda 6 daya kansa sabon angon Najeriyar yayi maza ya tunkara da zarar an rantsar dashi a matsayin shugaban ƙasa a Mayun 2023.

NESG ta saki hakan ne a wani rahoto data saki mai taken "Fahimtar Tattalin Arzikin Nijeriya: Mahimman Abubuwan daya kamata a Kula su ga Gwamnatin Mai shigowa"

Kara karanta wannan

Ashsha Shiri Ya Ɓaci: An Cafke Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi, An Tura Shi Kotu

Tinubu
Abubuwa 6 Da Tinubu Yake Buƙatar Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa
Asali: Depositphotos

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton yazo ne a watan Janairu 2023, inda yayi nuni zuwa ga manya manyan abubuwan da yakamata sabon shugaban ƙasa yayi ƙokarin tunkara babu ɓata lokaci.

Ƙungiyar da take mai rabin bada shawarwari akan manufofi na musamman kuma masu zaman kansu, sun lissafo batutuwan da ake buƙatar warwarewa cikin salon ujila waɗanda suka haɗa

Matsalar rashin aikin yi, gibin dake da akwai na kayan more rayuwa, raunin da kasafin kuɗi kan fuskanta, haɗi da giɓin ɗan adam da ƙwarewar fasaha, ƙarancin gine-ginen tsaro, da cin hanci da rashawa.

1. Rashin Aikin Yi da Talauci da Yayi Katutu a Ciki Ƙasa

Rashin aikin yi na daga cikin abin da ke ciwa Najeriya tuwo a ƙwarya. Rashin aikin da yayi katutu a ƙasa ne yasa ake fama da talauci mummuna. Saboda basu da abin kashewa.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Zata Soma Sauraren Koke-Koken INEC, Tinubu Atiku, da Obi

A wani rahoto da hukumar tattara alƙaluma ta NBS ta fitar, a Nuwamba 2022, tace aƙalla kaso 63 ciki 100 na yan Najeriya na fama da talaucin da yasa basu da asibiti, makarantu, yanayin rayuwa mai kyau, da tsaro.

Rahoton babban rahoto ne, domin ya haɗa da duk wani sashe na rayuwa a Najeriya.

Rahoton ya nuna cewa, kaso 33 cikin 100 na yan Najeriya basu da aikin yi, hakan na nuna Najeriya ita kaɗai ce ƙasa ɗaya tilo data fi kowacce ƙasa rashin aiki a cikin al'ummar ta.

2. Rashin Abubuwan More Rayuwa

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe da suke da naƙasu na ababen more rayuwa a duniya.

A matakin awo na ababen more rayuwa, Najeriya na mataki na 133 a cikin kasashe 140 na binciken da Global Competitiveness ta gabatar a 2019.

Lalacewa ta wutar lantarki, hakan ya kashe sana'o'i ƙanana. Wannan shine babban dalilin da yasa karatun koyon sana'ar nan na TVET ya samu tasgaro a makarantun mu.

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: APC Zata Miƙawa Yankin Igbo Shugabancin Majalisar Dattawa

Rashin wutar lantarki yasa kayayyakin da muke yi a gida cikin masana'antun mu ya ƙara kuɗi wanda haka ya zama tasgaro wajen cigaban su.

3. Gazawar Manufofin Kuɗi da Rashin Tasirin Su

Najeriya tana da mafi ƙarancin kuɗi da ɗan ƙasa yake samu na shiga hannun sa da 6-7%.

Najeriya ta dogara da man fetur ne, rashin tsadar da mai yake a kasuwar duniya da kuma yadda gwamnati bata iya amsar haraji yadda ya kamata.

Kashe kuɗi masu tarin yawa ga fannin tsaro tare da makuɗen kuɗaɗe ga ɓangaren gudanar da gwamnati.

Hakan yasa ake samun giɓi a kasafin kudin ko wacce shekara, har takai ga gwamnati na ciyo bashi. Yanzu a Najeriya, cin bashin gwamnati yanzu ya zama ruwan dare gama duniya da ake amfani dashi wajen tafikas da gwamnati.

Bashin da ake bin Najeriya yayi tashin gwauron zabi sau bakwai daga 2011 (triliyon ₦7.8) zuwa Triliyon ₦49.93 a farko farkon 2023.

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

Domin samun dawwamammen cigaban tattalin arziki, Tinubu ya tabbatar da ya ɗinke ɓarakar dake akwai dake sawa a samu giɓi a cikin kasafin kudi tare da kulle ɓarawar rance da gwamnati take.

Gami da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar faɗaɗa haraji zuwa wajen da a lokacin baya basa biya. Sannan ya tabbatar da cewar budget an yishi yadda aka tsara.

4. Arzikin Mutane Masu Cikakkiyar Lafiya da Zasu Iya Aiki Tare da Zaizayewar Kwararru

Abin ban haushi, Najeriya ya samu kanta a ƙasa a ƙiyasin Human Capital Index (HCI) na rashin kwararru. Abubuwan da suka haddasa haka kuwa nada alaƙa da rashi zuba jari a ilimi, ɓangaren lafiya da kuma rashin girbar albarkar da Allah yayi wa mutanen ƙasar nan.

Wannan dalili yasa ake samun yawan yara dake ajiye makaranta da kuma bautar da yara. Da yawa daga ƴan Najeriya sun gwammace su tafi wata ƙasar, musamman ma Turai da Amurka domin neman rayuwa mai inganci, har aka sama abin take da "Japa".

Kara karanta wannan

Sakamakon Zabe: Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta Kan Abu 1

5. Lalataccen Tsarin Tsaro

A shekarar 2021, Najeriya na matakin 146 cikin kasashe 163 na duniya a fannin tsaro alƙaluman Global Peace Index, kuma itace ƙasa ta takwas mafi ƙarancin tsaro a Afirka.

Abubuwa da yawa sun saka haddasa hakan, kama daga gurbacewar al'adu, rashin aikin yi, tazara tsakanin masu kuɗi da marasa kudi, talauci ya sa ayyukan laifi irin su sace mutane, kashe kashen mutane da fashi yayi kamari.

Hakan kuma ya samo asali ne abisa rashin kashewa fannin kudi, samar musu da kayan aiki.

6. Cin Hanci Da Rashawa da Yayi Katutu

Ci gaban da cin hanci da rashawa ya samu yana ci gaba da cutar ƙasar ta fannin handame dukiyar al'umma da masu madafin ido keyi.

Cin-hanci da rashawa a Najeriya ya haɗa da ƙarawa kudin kwangila kudi, cushe a kasafin kudi, almubazzaranci na kai tsaye, wanke kuɗin haram, cin hanci dana toshiyar baki, sace kudin gwamnati a wayance, ma'aikatan babu, lalata kayan aikin gwamnati cikin sani da sauransu.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

Da wannan yanayi na matsalar haraji, da kuma gibi a fasalin kuɗi na ƙasa da kuma cin hanci da rashawa da yayi katutu dole ne gwamnati taci gaba da samun tasgaro wajen aiwatar da ayyuka da suka shafi kuɗi.

Wasu daga cikin illolin cin hanci da rashawa ya haɗa korarar masu zuba jari a ƙasa, kashe masana'antu, tare da daƙile ci gaban tattalin arziki, gamida kawo koma baya fa yanayin rayuwa yan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel