Ku Mana Bayanin Dalilin Rashin Ɗora Sakamakon Zabe a Fotal, Kungiya Ga INEC

Ku Mana Bayanin Dalilin Rashin Ɗora Sakamakon Zabe a Fotal, Kungiya Ga INEC

  • Wata kungiya da ta kunshi fitattun 'yan Najeriya ta roki INEC ta fito ta yi karin haske kan zaben da aka kammala
  • Kungiyar ta nuna damuwa kan gazawar INEC wajen cika alkawarinta na amfani da fasahar zamani lokacin zaɓe
  • Tsoffin gwamnoni, tsoffin ministoci, Sanatoci da yan majalisar wakilai masu ci da waɗanda suka sauka duk suna cikin ƙungiyar

Tun bayan kammala zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya, kungiyoyi da wasu ɗaiɗaikun mutane suka fara sukar hukumar zaɓe kan yadda zaben ya gudana.

Wata kungiyar haɗa kan ƙasa da zaman lafiya ta bukaci hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta fito ta yi wa yan Najeriya gamsasshen bayani kan abinda ya faru ranar Asabar.

Hukumar zabe INEC.
Tambarin hukumar zabe ta ƙasa INEC Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta tattaro cewa ƙungiyar ta kunshi fitattun yan Najeriya da suka haɗa da tsoffin gwamnoni, tosffin ministoci, mambobin majalisun tarayya masu ci da waɗanda suka sauka, shugabannin matasa da sauransu.

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Bayan wani taro da suka gudanar a Abuja, ƙungiyar ta ce akwai bukatar INEC ta sanar da 'yan Najeriya komai domin guje wa maimaita abinda ya auku a wancan zaben ranar 11 ga watan Maris.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jawabi ga 'yan jarida a Abuja ranar Jumu'a, tsohon ɗan majalisa kuma sakataren ƙungiyar, Dakta Cairo Ojougboh, ya bukaci shugabannin jam'iyyu su sasanta saɓanin da ya shiga tsakaninsu lokacin zaɓe.

Ya ce taron da suka gudanar ya maida hankali ne kan sakamakon zaben shugaban ƙasa da yan majalisu, da kuma wasu batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ƙasa.

Ƙungiyar ta ce:

"INEC ta yi kokarin inganta zaɓe a Najeriya domin tabbatar da sakamako bai zo da matsala ba. Kamar sauran yan Najeriya, mun damu da cewa INEC ta gaza cika alƙawurranta na amfani da fasaha musamman tura sakamko ta Intanet."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kama Ɗan Majalisar Tarayya Na NNPP da Bindiga a Kano

"Taron mu ya cimma matsaya kan cewa muna bukatar INEC ta yi bayai game da wannan tasgaro da aka samu da kuma matakan da ta ɗauka don kaucewa haka a zaben gwamnoni mai zuwa."
"Zaben shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya ya gudana lami lafiya, ƙungiyar mu ta yaba wa masu kaɗa kuri'a da suka fito sauke hakkinsu. Muna kira kowa ya kwantar da hankali har a miƙa ragama hannun sabuwar gwamnati."

A nasa jawabin, Sanata Ita Enang, ya yaba wa kasashen duniya bisa yadda suke taya Najeriya da zababben shugaban ƙasa murna bisa nasarar da ya samu a zabe.

Sanatan ya ƙara da cewa kalaman da kasahen ke aiko wa wani karin kwarin guiwa ne ga hukumar zaɓe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ban da Masaniyar Tinubu Na Yunkurin Neman Sulhu, Atiku

A wani labarin kuma Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce bai da labarin Tinubu na shirin neman sasanci

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Peter Obi Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Ci Zabe, Ya Yi Alkawarin Abu 1 Tak

Yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon zaben shugaban kasa, ɗan takarar na PDP ya ce zai nufi Kotu domin shi ne ya samu nasara.

Haka na ya bayyana matakin da zai ɗauka na gab idan har Kotu ta gaza kwato masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel