Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ya Shiga Hannun Hukuma

Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ya Shiga Hannun Hukuma

  • Wani soja mai safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Legas ya gurfana a gaban kotu domin girbar abinda ya shuka
  • Lauyan hukumar NDLEA yace wanda ake ƙarar ya dade yana aikata wannan baƙar sana'a ta safarar miyagun ƙwayoyi
  • Sai dai, wanda ake zargin ya musanta dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su a gaban kotun

Jihar Legas- An gurfanar da wani soja mai shekara 49 a duniya mai suna Olanrewaju Lawal, a gaban wata babbar kotun tarayya a jihar Legas bisa zargin sa da shigo da ƙwayar tramadol da wasu haramtattun ƙwayoyi a jihar.

Lawal wanda aka gurfanar da shi a gaban mai shari'a Akintayo Aluko, yana fuskantar tuhume-tuhume shida kan cin amana da safarar haramtattun ƙwayoyin ba bisa ƙa'ida ba. Rahoton The Punch

NDLEA
Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ya Shiga Hannun Hukuma Hoto: The Punch
Asali: UGC

Lauyan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA), Lambert Nor, ya gayawa kotu cewa wanda ake ƙarar da wasu waɗanda suka gudu, sun daɗe suna safarar miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan

Zagon Ƙasa: An Gurfanar Da Wani Ma'aikaci Gaban Kotu Bisa Sama Da Faɗi Da Miliyoyin Kuɗaɗen Kamfani

Yace sun yi safarar ne a tsakanin 15 ga watan Satumban 2022 zuwa 12 ga watan Janairun 2023, lokacin da aka cafke shi a Ago Palace Way, Okota, jihar Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nor ya gayawa kotun cewa wanda ake ƙarar an cafke shi dauƙe da haramtattun kayan masu yawa waɗanda suka haɗa da Tramadol hydrochloride 250mg mai nauyin kilogiram 223.65.

Sauran ƙwayoyin sune Tramadol hydrochloride 225mg mai nauyin kilogiram 28.40; Pregabalin mai nauyin kilogiram169.4 kilograms, da Codeine mai yawan lita 1,469

Sai dai, wanda ake ƙarar ya ƙi amsa tuhume-tuhumen da ake masa. Rahoton TVC News

Bayan ya ƙi amsa laifukan da ake tuhumar sa da su, sai mai shigar da ƙara ya buƙaci kotu da ta sanya ranar fara shari'a sannan ta sakaya shi a gidan gyaran hali.

Alƙalin kotun, Aluko, bayan ya saurari lauyoyin biyu, ya bayar da umurnin a tsare wanda ake ƙarar a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

An Tsinci Wani Mutum Da Aka Yi Wa Fashin N97,000 A Sume A Gefen Titi Da Kebur A wuyansa A Jigawa

A wani labarin na daban kuma, an tsinci wani mutum sume a gefen titi bayan an yi masa fashi da makami.

Mutumin dai an tsince shi ne yashe a gefen titi da kebur a wuyan sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel