Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar Labour Ya Janye Daga Takara, Ya Bar Wa Binani Ta APC

Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar Labour Ya Janye Daga Takara, Ya Bar Wa Binani Ta APC

  • Dan takarar gwamnan LP a jihar Adamawa ya bayyana janyewa daga takarar tare da marawa ‘yar takarar gwamnan APC
  • Otumba ya ce, shi da Aishatu Binani suna da manufa iri daya, don haka ya dace su hada kai don ci gaban jihar
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da shirin zaben gwamna a fadin jihohin Najeriya a ranar 11 ga watan Maris

Jihar Adamawa - Dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour na jihar Adamawa, Umar Mustapha ya bayyana janyewa daga takara tare da marawa Sanata Aisha Ahmad Binani baya.

Binani ce ‘yar takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Adamawa da ke Arewa masu Gabashin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Kwanaki biyu kafin zaben shugaban kasa, Mustapha ya zargin jam’iyyar Labour da kitsa yadda za ta kada shi, inda ya bayyana nesanta kansa da Peter Obi tare da kiran mabiyansu su zabi Tinubu na APC.

Kara karanta wannan

N30k duk wata: Dan takarar gwamna ya fadi abu 2 da zai yiwa matasa idan aka zabe shi

Dan takarar LP ya janyewa Binani a Damawa
Sanata Aisha Binani, 'yar takarar gwamnan jhar Adamawa a APC | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Da yake zantawa da masu ruwa da tsaki na APC a ranar Lahadi, Mustapha da aka fi sani da Otumba ya bayyana janyewa Binani takarar gwamnan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muna da ra'ayi iri daya

A cewarsa, Binani na da ra’ayin ciyar da al’ummar jihar gaba kamar yadda shi ma ya dauko aniyarsa a tun farko, NewsWire ta tattaro.

A cewarsa:

“Ni Mustapha Otumba, dan takarar gwamnan jam’iyyar Labour na janye daga takarar gwamna don marawa Sanata Aishatu Ahmed Binani baya.
"Mu biyun duka mun gano cewa muna da hange iri daya kuma cewa mutane suna farin cikin zamu raba kuri’unmu.
“A yanzu mun hada kai kuma ina kira ga magoya bayana, matasa da tsofaffi, maza da mata da su fito kwansu da kwarkwata a ranar 11 ga watan Maris domin zaban Aisha Ahmad Binani a matsayin gwamna.”

Kara karanta wannan

Ku taimake ni: Gwamnan PDP ya yi murya kasa-kasa, ya roki mata alfarma a zaben ranar Asabar

Ka yanke shawari mai kyau

Da take martani ga batun nasa, Binani ta yaba da wannan mataki na Otumba, inda ta yi kira ga sauran jam’iyyun siyasa da su yi koyi dashi.

Otumba na daya daga cikin mutum biyar da Binani ta kayar a zaben fidda gwanin gwamnan jam’iyyar APC a jihar ta Adamawa.

A baya kun ji cewa, tsohon gwamnan jihar Anambra ya shawarci Peter Obi na jam'iyyar Labour kan ya janye daga takarar shugaban kasa.

Dan takarar na Labour haka ya fadi a zabe warwas bayan yin biris da shawarin da tsohon gwamnan ya bashi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel