"Mijina Yana Son Na Bayar Da Ƙoda Ta Ga Mahaifiyar Sa", Matar Aure Ta Koka

"Mijina Yana Son Na Bayar Da Ƙoda Ta Ga Mahaifiyar Sa", Matar Aure Ta Koka

  • Wata matar aure ta bayyana halin da rayuwar auren ta take ciki ita da mijinta da kuma surikar ta
  • Matar auren ta bayyana cewa mijinta yana son ta bayar da ƙodar ta domin a dasawa mahaifiyar sa
  • Matar wacce matashiya ce ta ƙi yarda da hakan, sannan ta bayyana dalilan ta na ƙin yarda da wannan roƙon nasa

Wata matar aure mai shekara 25 a duniya, mai suna Folake, ta bayyana halin tsaka mai wuya da ta tsinci kanta dangane da rashin lafiyar surikar ta.

Ta bayyana cewa mijinta mai shekara 35 a duniya yana roƙon ta bayar da ƙodar ta ga mahaifiyar sa saboda sun zo iri ɗaya. Shafin Yabaleftonline ya rahoto.

Mata da miji
"Mijina Yana Son Na Bayar Da Ƙoda Ta Ga Mahaifiyar Sa", Matar Aure Ta Koka Hoto: Yabaleftonline
Asali: UGC

Sai dai, matar ta nuna damuwar ta, kan cewa duk da alaƙar dake akwai a tsakanin su da mahaifiyar ta sa, shekarun ta sun yi kaɗan ace ta bayar da ƙodar ta.

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Folake ta kai kukan ta soshiyal midiya domin neman shawarwari kan ko tayi kuskure da ta ƙi yarda ta bayar da ƙodar ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta:

"Shekara ta 25 a duniya. Ina auren ɗan shekara 35. Mun fi shekara biyu muna zaman aure sannan muna yaro ɗaya. Abinda ya kawo ni nan shine surikata bata da lafiya (ciwon ƙoda) sannan tawa tayi daidai da ta ta.
"Mijina yana roƙona na bayar da ɗaya daga cikin ƙoda ta domin a ceto mahaifiyar sa. Yace yana ƙaunar ta sannan baya son wani abu ya faru da ita. Yace yanzu lokaci yayi da zan nuna son da nake cewa ina yi masa.
"Na ƙi yarda na bayar."
"Ta yaya yarinya ƙarama kama ta wacce yanzu ta fara rayuwa zata bayar da ƙodar ta ga wata tsohuwa mai shekara 48 a duniya. Yanzu mijina yana ta min wani gani-gani. Yana cewa idan wani abu ya samu mahaifiyar sa,

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Yunwa Da Hare-Hare Yasa Sun Koma Sace Mutane Tare Da Neman Kudin Fansa

"Ba zai taɓa yafe min ba. Shin don Allah nayi mugunta?"

"Cewa Yayi Na Kawo Kuɗi" Amarya Ta Fasa Aurenta Ana Saura Mako Ɗaya Biki

A wani labarin na daban kuma, wata amarya ta watsawa angon ƙasa a ido ana saura sati ɗaya a ɗaura musu aure.

Amaryar ta bayyana dalilin da ya sanya tayi hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel