"Cewa Yayi Na Kawo Kuɗi" Amarya Ta Fasa Aurenta Ana Saura Mako Ɗaya Biki

"Cewa Yayi Na Kawo Kuɗi" Amarya Ta Fasa Aurenta Ana Saura Mako Ɗaya Biki

  • Wata budurwa ta fasa aurenta saboda kawai wanda zata aura ya nemi wata alfarma a wajenta
  • Angon ya nemi amaryar da ta ɗan kawo abinda ya samu domin a taru a kashe mahaukacin kare wajen yin bikin su
  • Amma ina sai kawai ta tubure tace ko sisi ba zata saka ba inda daga ƙarshe tace Allah haɗa kowa da rabon sa

Shagulgulan da ake gudanarwa a wajen bikin aure na ƙayartawa matuƙa, amma sai dai a wani lokacin rashin kuɗi a hannun ma'auratan na kawo hatsaniya.

Wani labari da wani mai amfani da sunan @dexterouz11 a Twitter, ya sanya ya ɗauki hankulan mutane da dama waɗanda suka yi mamakin abinda ya faru.

Amarya
Cewa Yayi Na Kawo Kuɗi" Amarya Ta Fasa Aurenta Ana Saura Mako Ɗaya Biki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wani mai shirin zama ango ne ya nemi wacce zai aura da ta taimaka ta kawo gudunmawarta domin bikin auren su wanda zai zo nan da mako ɗaya.

Kara karanta wannan

Gamo Da Katar: Budurwa Ta Fashe Da Kukan Daɗi Bayan An Gwangwajeta Da Miliyoyi

Angon ya nemi kawai amaryar da ta ɗan tallafa da abinda ya samu koda ba mai yawa bane, wanda bai wuce ɗan lemun da da zaa sha ba a wajen bikin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amaryar tace sam ba zata sanya ko ƴar ficikarta ba a wajen bikin inda daga ƙarshe tace ta fasa auren ana saura sati ɗaya a ɗaura musu aure.

Rubutun da @dexterouz11 yayi na cewa:

"Wannan babban magana ce mai matuƙar muhimmanci ooo. Wata budurwa tace ta fasa aurenta ana saura mako guda saboda wanda zata aura ya nemi da ta ɗan tallafa da duk abinda ya samu domin a gudanar da bikin."
"Yace ta ɗaure ko da kuɗin lemun da za a sha ne ta biya. Kawai sai tace ta fasa aure."

Kukan Daɗi: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Samu Kyautar Maƙudan Kuɗi

Kara karanta wannan

Na Fasa Auren: Amarya Ta Fusata Bayan Ta Gano Babban Sirrin Da Ango Da Babbar Ƙawarta Suka Ɓoye Mata

A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta samu abinda bata taɓa zata ba inda aka gwangwaje ta da kyautar miliyoyin kuɗaɗe.

Kamar daga sama haka budurwar taji labarin kyautar miliyoyin kuɗin wanda saboda murna da farin ciki har kukan daɗi ta ɓarke da shi.

An bayyana cewa wani abin alheri da ta yine a baya ya sanya ta samu kyautar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel