Da ɗumi ɗumi: Boko Haram Sunyi Awon Gaba da Wasu Matafiya Guda 7

Da ɗumi ɗumi: Boko Haram Sunyi Awon Gaba da Wasu Matafiya Guda 7

  • Yan Boko Haram na cigaba da addaban al'ummar Arewa maso gabas musamman jihar Borno
  • Wannan na faruwa duk da wutar da dakarun sojin Najeriya ke musu a tafkin Chadi da dajin Sambisa
  • Yanzu lamarin ta'addancin ya dau sabon salo inda suke garkuwa da mutane don karbar kudin fansa

Borno - Duniya ina zaki damu ne. Ana batu na siyasa sai kuma batun harin ƴan ta'adda ya sawo kai, a wani salo na "an daɗe ba'a gamu ba".

Magana ake na wani hari da ƴan kungiyar Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l Jihād da aka fi sani da Boko Haram suka ƙaddamar wa wasu matafiya, ƴan mintuna da suka wuce.

Mayakan masu iƙirarin yin jihadi, sun farmaki wasu matafiya ne a cikin Magumeri ta Barno, sannan suka yi awon gaba da 7 daga cikin matafiyan.

Kara karanta wannan

Za'a Sake Gina Ƙonanniyar Kasuwar Maiduguri Ta Monday Market Daga Makon Nan - Zulum

Zulum
Gwamna Zulum da Sojoji da Yan sanda Hoto: GovBorno
Asali: Facebook

Tunda da fari dai, wani rahoto da jaridar Leadership ta ruwaito baya bayan nan ya nuna cewa, ƴan ta'addan sun dirar wa ƙauyen Ngamma ne a ranar Alhamis ɗin data gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ƙauyen na Ngamma, sun samu nasarar cafke mutane da basuji ba basu gani guda uku, tare da mata huɗu ta hanyar yi musu kule da bindiga.

\Koda Zagazola Makama, mai ilimi a fannin Tsaro kuma mai sharhi akan Yanayin tsaro a lardin tafkin chadi, yace waɗanda aka sacen anyi da su ca ƴankin Gudumbali ne.

Majiyar Leadership Jarida ta ƙara da cewa, maharan sun buƙaci iyalai da ƴan uwan waɗanda aka sace da su bada kuɗin fansa.

Wani jami'in tsaro daya buƙaci a ɓoye sunansa daya tabbatarwa da majiyar mu faruwar lamarin yace Boko Haram na fuskantar yanayi na yunwa da wahalar gaske saboda jerin haraharen da jaruman zaratan sojojin Najeriya ke kai musu haɗi da yaƙin cikin gida da ƙungiyar ke fama dashi.

Kara karanta wannan

A Kwantar Da Hankali, Kada a Kaiwa Igbo Hari, Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Wanda saboda wadannan dalilai ne majiyar tamu tace, yasa Boko Haram ta koma sace mutane tare da neman kuɗin fansa.

Fiye da yan Boko Haram 300 ne suka miƙa wuya a hannun sojojin Najeriya dake Mafa, Konduga da Bama a cikin satin daya shuɗe.

Hakan na zuwa ne bayan da Sojojin suka ragargaji wani babban sansanin da ƴan boko haram suke da ƙarfi sosai a Gaizuwa wanda ake kira da Mantari, Gabchari da Maimusari duka a cikin ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

Jim Kadan da Yin Zabe Bankuna na Cigaba da Amsar Tsofaffin N500 da N1000

A wani yanayi na kamar jira ake agama zaɓen Shugaban ƙasa, rahotanni na nuna bankuna sun dawo amsar tsofaffin kuɗaɗe ₦500 da ₦1000 a hannun mutane.

Duk da cewa CBN ya nace akan cewa bai bada umarni ga bankuna suci gaba da amsar tsofaffin Kuɗaɗen a hannun mutane ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

Wani babban jami'i a CBN yace, jita jita ce kawai amma CBN ne yabada umarnin amsar tsofaffin kuɗaɗen na N500 da N1000.

Inda yace CBN yace, mafi yawan abinda za'a iya amsa a wajen mutum bazai wuce N500,000 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel