Hukunci 6 da Kotun Koli ta Zartar Game da Tsarin Canza Takardun Kudi a Najeriya

Hukunci 6 da Kotun Koli ta Zartar Game da Tsarin Canza Takardun Kudi a Najeriya

  • Kotun koli ta zartar da hukunci cewa canza takardun kudi da bankin CBN ya yi, ya sabawa ka’ida
  • Mai shari’a Inyang Okoro ya jagoranci zaman da kotun koli tayi a ranar Juma’a, 3 ga watan Maris 2022
  • Daga cikin hukuncin da kotu ta zartar shi ne canjin kudin ya sabawa dokar da ta kafa bankin CBN

Duka Alkalan da suka saurari shari’ar sun hadu kan hukuncin da aka zartar, suka ce an saba doka da aka hana aiki da N200, N500 da N1000.

Abubakar Sadiq Usman wanda Hadimi ne ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Lawan, ya jero hukuncin da kotun koli ta zartar.

Hadimin da aka sani da Mr. Abu Sidiq ya jero hukuncin ne a shafinsa na Twitter.

1. Kashe tsofaffin takardun N200, N500 da N1000 da aka yi, ya sabawa dokar da ta kafa babban bankin CBN.

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

2. Mai girma Shugaban kasa ba zai iya daukar wani mataki shi kadai ba tare da hadin-kan Gwamnonin Jihohi ba.

Majalisa
Majalisar magabata ta kasa Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Wajen daukar wannan mataki, ya wajaba Shugaban kasa ya yi aiki tare da majalisar magabata na Kasa.

4. Tsarin da aka fito da shi na canza wasu manyan takardun kudi ya tauye hakkin Gwamnatocin Jihohi.

5. Umarnin da Mai girma Shugaban Najeiya ya bada na hana amfani da N500 da N1000 ya ci karo da dokar kasa.

6. Za a cigaba da amfani da tsofaffin Nairori a matsayin takardun kudi har zuwa 23 ga watan Disamba 2023.

Dalilin canza kudi

A baya an ji labari cewa Shugaban Najeriya ya ce an canza takardun kudi ne domin farfado da tattalin arziki kasa ba da wata manufa ba.

A wani jawabi, Muhammadu Buhari ya roki a zabi duk ‘yan takaran APC a zaben Jihohi da yake tallatawa ‘Yan Kaduna Sanata Uba Sani.

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

Asali: Legit.ng

Online view pixel