Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa
- Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga mutanen jihar Kaduna yayin da ake shirin yin zaben Gwmanoni
- Shugaban kasar ya ce an canza takardun kudi ne domin farfado da tattalin arziki kasa ba wata manufa ba
- A karon karshe kafin ya bar ofis, Buhari ya nemi alfarma wajen al’ummar Kaduna da za su zab masa APC
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ba mutanen Najeriya hakuri a game da tsarin canza takardun kudi da gwamnatinsa ta amince ayi.
The Cable ta rahoto Muhammadu Buhari yana mai cewa babban bankin CBN bai fito da wannan tsari saboda a jefa al’umma a cikin wahala ba.
A wani bidiyo da Uba Sani ya daura a shafinsa na Twitter, an ji shugaban kasar yana neman afuwa a kan halin da Bayin Allah suka samu kan su.
Sanata Uba Sani shi ne ‘dan takarar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, zai kara da Isa Ashiru Kudan a zaben mako mai zuwa.
Mutanen Kaduna su yi APC sak
Legit.ng Hausa ta saurari wannan gajeren bidiyo, an ji shugaban Najeriyan yana mai neman afuwa tare da yin kira da a sake zaben APC a Kaduna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari ya yabi Uba Sani, ya ce ‘dan takaran zai taka rawar gani idan aka ba shi dama, sannan ya roki a zabi sauran ‘yan takaran na jam’iyya mai-ci.
Kira ga 'Yan Kaduna
"Assalamu Alaikum ya ku jama’an jihar Kaduna. Da farko ina kara godiya ta musamman da yarda da kuka yi da ni, ku ka zabe ni har sau biyu a matsayin shugaban kasa a jam’iyyarmu ta APC.
Zan yi amfani da wannan damar domin in sanar da ku cewa Sanata Uba Sani ya nuna kwazo da jarunta, zai yi rawar gani In sha Allahu, fiye da yadda ake tsammani.
Ina ba ku hakuri a kan wahalar da aka sha ta canjin kudi, an yi don tattalin arzikin kasa, ba don wasu su wahala ba.
Kaduna gida ce a gare ni, ku fito ku zabi Sanata Uba Sani da duka ‘yan takaranmu na APC. Ayi zabe lafiya. Nagode kwarai da gaske."
- Muhammadu Buhari
An yi wa APC makarkashiya
A jiya aka samu labari Gwamnan Jihar Katsina ya bada umurnin tsigewa da canza wasu kwamishinoni da sakatarori saboda sun yi wa APC zagon-kasa.
Alhaji Bashir Gambo Saulawa ya canji Alhaji Usman Nadada, shi kuma ya koma ma’aikatar ƙasa da sifiyo, Sani Ɗanlami ya zama Kwamishinan wasa.
Asali: Legit.ng