Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara

Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara

  • A Sakon, Bola Tinubu Ya Ambaci Sunan Atiku, Kwankwaso da Obi a Wani Salo na Dannar ƙirji
  • Tinubu Yace, Tunda Ake Gudanar da Zaɓe, Ya Ɗauki Duka Ukun A Matsayin Ƴan Uwan sa, Kuma Abokan sa
  • A Miƙa Musu Hannun Gayyatar Abokantaka Domin Ɗaura Najeriya Akan Turbar da Duk Wani Ɗan Ƙasar Zaiyi Alfaharin Kiranta da Kasarsa

Duk a cikin yanayi murna da ayyana shi da INEC tayi a matsayin wanda yaci zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aike saƙo mai nuna ƴan uwantaka ga abokan hamayya sa a zaɓen daya wuce.

Yayi ga ga babban abokin hamayyar sa mafi ƙarfi Alhaji Atiku Abubakar daya zo su haɗu waje guda domin kai Najeriya tudun muntsira.

Kara karanta wannan

Kada Ka Kuskura Ka Haɗa Gwamnatin Haɗaka Inji Tanko Yakasai Ga Tinubu

Tinubu
Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bugu da ƙari, bai gushe ba anan domin sai da Tinubu yayi kira ga Peter Obi na Labor Party tare da Rabi'u Musa Kwankwaso na NNPP suka zo na uku dana huɗu da kasa suyi ƙasa a gwuiwa wajen amsa kiran kai Najeriya zuwa tudun mun tsira.

A cewar Tinubu kamar yadda Legit ta ruwaito :

"Nagodewa Allah madaukakin sarki, abisa jin ƙansa, da yayi Ni a matsayin ɗan Najeriya, domin samun wannan babbar dama na zama mai nasara a cikin zaɓen nan. Ina fatan ya bani karfin gwuiwa waje jagorantar wannan ƙasa zuwa tudun mun tsirar daya tsara zata kai.
"Daga ƙarshe, ina godewa yan Najeriya abisa nuna goyon bayan su ga demokradiyyar mu. Zan yi muku adalci yan Najeriya. Zanyi abinda kuke so, ku shirya domin girbar kabakin alkairi da zakuyi alfahari da Najeriya a matsayin ƙasar ku.

Kara karanta wannan

Yan Watanni Bayan Rabuwa Da Matarsa Da Kuma Musulunta, JJC Skillz Yayi Aure A Kano

" Ga abokan hamayya ta, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku, Tsohon gwamna Kwankwaso, da Tsohon gwamna Obi, Ga tayin abota na miƙo muku. Tabbas ansha gumu wajen neman nasara.
Ina mai matuƙar girmama ku". inji shi.

Sannan ya rufe da:

" Lokacin zaɓen da akai, abokan hamayya tace, amma ba abokan gaba ba. A zuciya ta, ƴan uwana nane ku."

Wata Mata Tayi Bilicin a Baya Ta Tuba, Tace Tayi Nadamar Yin Sa

Matar data ga yadda fatar ta koma babu kyau, tace tayi nadamar yin haka kuma da wuya ta sake yi.

Diyar matar ce sanadin nadamar, inda bayan taga hotunan daurin auren tane taganta baƙa duwul.

Amma kuma yanzu ta koma fari. Matar ta amsa mata da cewa tayi dana sanin yin bilicin lokacin da take budurwa.

Tace ta saki layin bilicin bayan ta fahimci ba mai ɓullewa bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel