"Maza Basa Ɓata Lokaci " Ƴan Watanni Bayan Rabuwar Su Da Funke Akindele, JJC Skillz Yayi Aure A Ɓoye

"Maza Basa Ɓata Lokaci " Ƴan Watanni Bayan Rabuwar Su Da Funke Akindele, JJC Skillz Yayi Aure A Ɓoye

  • Sanannen jarumi a masana'antar fim ta Nollywood, kuma tsohon Mijin Funke Akindele JJC Skillz, Yayi Aure Sirri Shida Wata Masoyiyar sa
  • Rahotanni sun ce, mai shirya waƙoƙin, ya Auri Wata Ƴar Ƙabilar Egbira ne a Garin Kano Watanni Ƙadan da Rabuwar su da Funke
  • Bayan rabuwarsa da Funke ya sanar da cewa ya koma addinin Musulunci

Soyayya kenan, watarana tayi ƙarko Wata rana kuma ta zaizaye kamar yadda kyandir ke cin wuta yayin da aka kunna.

Rahotannin na cewa sanannen mai shirya waƙoƙin nan da aka fi sani da JJC Skillz, tsohon miji ga jarumar fina finan Nollywood ɗin Najeriya, Funke Akindele ya angwance a sirrance a Kanon dabo.

Shahararren mawallafi a yanar gizo gizo Tosin Silverdam ne ya ruwaito cewar, JJC Skillz yayi auren ne bayan ya haɗu da wata ƴarinya ƴar ƙabilar Egbira dake zaune a Kano yar asalin jihar Kogi, mai suna Falilat.

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara

Funke
"Maza Basa Ɓata Lokaci " Ƴan Watanni Bayan Rabuwar Su Da Funke Akindele, JJC Skillz Yayi Aure A Ɓoye Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bai tsaya anan ba, mawallafin ya ƙara da wallafa hotunan ɗaurin auren. Amma ba tare da hotunan Skillz ba, saboda yaƙi yarda a ɗauki hotunan sa a wajen ɗaurin auren.

Amma duk da hakan vidiyon matar tasa ya karaɗe kafafen sadarwa na zamani a ranar ɗaurin auren.

Kalli Bidiyon Yadda Lamarin Bikin Ya Wakana:

Ɗaurin Auren na JJC Skillz na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan auren sa da Funke Akindele yazo ƙarshe.

Idan za'a iya tunawa, a watan Yuli na 2022 ne ya sanar a Yanar Gizo Gizo cewar shida tsohuwar matar tasa sun raba gari, bayan duk wani ƙoƙari da sukayi domin ɗinke ɓaraka tsakanin su ya haɗu da tasgaro.

Ƴan Najeriya Sun Tattauna Akan Batun Ƙara Auren JJC Skillz Tsohon Mijin Funke Akindele, Bayan Rabuwa ta Yan Lokuta.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Gwabnonin 6 Da Suka Fadi Zaben Zama Sanatoci A Zaɓukan 2023

Yanayin yadda JJC Skillz yayi maza yayi wuff da wata, ya manta da tsohuwar matar sa ya janyo musayar yawu da shauƙi kala kala.

Ga Kaɗan daga ciki:

tiana_hairport_and_more:

"Wayyo, abin yayi sauri, Inda ace mace ce tayi, ba za'a barta ta sarara ba."

Ita kuwa _bettygotbetter cewa tayi

"Wai me yasa suke saurin aure ne haka! Ina nufin me yasa waɗanda suka rabu suke saurin ƙulla wani alaƙar aure?

Jiddahkhan:

"JJC Skillz ya daɗe a Abuja, hakan na nufin gaskiya ne batun".

queen_deb_orville:

“Hakan na nuna cewar, ya daɗe yana cutar da auren su...Ku duba fa, a ƙasa da shekara ɗaya har mutumin nan ya auri wata mata ba tare da yayi kokarin ɗinke ɓarakar alaƙar dake tsakanin su da tsohuwar matar ba. Kuda kuke tsayawa shekara 3 zuwa 4 kuna jira soyayyar ku tayi ƙarfi kuna dai gani ko? A wata nawa ya gamu da matar, ya afka son ta, har ya aure ta."

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

hardey_hardey:

“Yanzu da ace Funke Akindele ce ta ƙara aure watanni kaɗan bayan rabuwar su da mijin ta, da yanzu surukai na yanar Gizo Gizo suna nan suna mata saukale".

Cabeerah:

"Ku dai ci gaba da yarda da maza ".

Aubiergembock:

"Ku tsoraci maza. Ina nanatawa, Kuji Tsoron Maza. Na baya da basa ji, Nace Kuji Tsoron Maza."

only1mathair kuwa cewa tayi:

"Maza yanzu zasu bata maka rayuwar ka ta farin ciki".

Mayakan Boko Haram Shigar Mata Suke Yi Yayin Kai Hari

Sanata Ali Ndume ya bayyana wasu dabaru da mayakan Boko Haram ke amafani da shi wajen kai hare-hare. Ndume ya ce yanzu samfarun dabarun da mayakan kungiyar ta'addancin suka koma yi shine sanya tufafin mata yayin kaddamar da hare-hare a garuruwan Borno.

Ya taya zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima murnar cin zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel