Matar Da Tayi Bilicin a Baya Ta Tuba, Tace Tayi Nadamar Yin Sa

Matar Da Tayi Bilicin a Baya Ta Tuba, Tace Tayi Nadamar Yin Sa

  • Wata mata ta nuna yadda kamannin fatar jikin ta yake a baya lokacin da take yin bilicin ba ƙaƙƙautawa
  • A cikin bidiyon da ya yaɗu a TikTok, matar ta kuma nuna yadda kamannin ta suke yanzu da ta tuba ta daina bilicin
  • Matar ta kuma shawarci ƴan'uwan ta mata da su kiyayi yin bilicin saboda gagarumar illar da yake da ita

Bidiyon wata mata wacce ta tuba ta daina yin bilicin ta koma kalar fatar jikinta ta ainihi, ya ɗauki hankula sosai.

Ɗiyar matar dai itace ta tambaye ta bayan ta ga hotunan aurenta inda ta lura da yadda kalar fatar jikinta tayi haske.

A cikin bidiyon wanda @dengajith91, ya sanya, yarinyar ta ga hotunan auren mahaifiyar ta inda ta tambaye ta dalilan da ya sanya tayi bilicin.

Mai bilicin
Matar Da Tayi Bilicin a Baya Ta Tuba, Tace Tayi Nadamar Yin Sa Hoto: TikTok/dengajith91
Asali: UGC

Matar ta amsa mata da cewa tayi dana sanin yin bilicin lokacin da take budurwa. Tace ta saki layin bilicin bayan ta fahimci ba mai ɓullewa bane.

Kara karanta wannan

Ina Mazan Suke: Saurayi Nake Nema Ruwa a Jallo, Samari Tsorona Suke Ji, Kyakkyawar Soja Ta Koka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta kuma shawarci mata da su daina yin bilicin saboda illar da yake da ita.

Bidiyon ya kuma nuna yadda kamanninta suke lokacin da take amfanin man bilicin. Fatarta tayi haske a lokacin.

Sai dai, yanzu angulu ta koma gidanta na tsamiya domin kalar fatarta ta dawo baƙa.

Bidiyon ya yaɗu sosai

Bidiyon ya janyo mutane da dama da suka kalle shi a TikTok, tofa albarkacin bakin su.

Ga kaɗan daga ciki:

@1738488ahwu1816 ya rubuta:

"Kin ci sa'a kalar fatar ki ta dawo daidai sannan baki kamu da cutar kansa ba. Wasu mutanen suna da sa'a sosai. Naji daɗin yadda kike son kalar fatar ki yanzu."

@Siwa ta rubuta:

"Kina da kyau sosai."

@Aïcha Ali ta rubuta:

"Kin yi kyau sosai, gaskiya baƙi ado ne sosai."

@Gracieee.c ta rubuta:

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Layin Zabe a Zamfara

"Kina da kyau sosai, ya matuƙar birge ni."

@Aniya ta rubuta:

"Na taya ki murna kalar fatar ki ta dawo yadda take, gwanin kyau."

@Lily ta rubuta:

"Lallai kin isar da saƙo mai muhimmanci."

Matashiyar Sojan Najeriya Ta Koka Kan Rashin Saurayi, Tace Samari Tsoronta Suke Yi

A wani labarin ma daban kuma, wata matashiyar soja ta koka kan rashin saurayi, tace maza tsoron ta suke ji.

Bidiyon matashiyar sojan ya ɗauki hankula sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel