Dan Sanda Ya Yi Wa Likita Mugun Duka A Kwara Saboda Ya Duba Matarsa Ba Da Izininsa Ba

Dan Sanda Ya Yi Wa Likita Mugun Duka A Kwara Saboda Ya Duba Matarsa Ba Da Izininsa Ba

  • Dan sanda ya yi wa likita rauni bisa zargin kin neman izinin sa kafin duba matarsa a Ilorin
  • Bisa wannan dalilin kungiyar likitoci reshen babban asibitin Illorin a jihar Kwara sun shiga yajin aikin kwanaki biyu
  • Hukumar asibitin da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Kwara sun yi alwashin daukar matakan da ya dace don kare faruwar haka nan gaba

Ilorin Kwara - Mambobin kungiyar likitocin gwamnati da likitocin hakori na babban asibitin Illorin, Jihar Kwara, sun gudanar da yajin aikin kwana biyu saboda zargin cin zarafin abokin aikin su, rahoton The Punch.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa shugaban kungiyar likitoci ta kasa reshen, Dr Ola Ahmed, ya ce an tilasta wa likitocin ajiye kayan aiki saboda yawan yin barazana ga rayuwarsu.

Asibiti
Kofan shiga babban asibitin Ilorin. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

''Bayan taron gaggawa, likitocin sun yarda babu wani likita da zai yi aiki a asibitin na awanni 48. Mun gaji da rashin da'ar da mutane ke mana'', a cewarsa.

Ahmed ya bayyana cewa wani sajan din rundunar yan sanda ya ci zarafin wata likita a babban asibitin.

Ya yi bayanin cewa da misalin karfe 5:00 na yammacin Lahadi, an ci zarafin a likitar da ke sashen kula da matsalolin mata, a hannun wani sajan din dan sanda da ya kawo matarsa a duba ta.

Dalilin da yasa sajan ya yi wa dan sandan duka

Ya ce:

''Likitan ya gudanar da duk wani gwaji da ya zama dole kuma ya sallami matar. Sajan din, daga baya, ya dawo asibitin ya kuma farmaki likitan da ya duba matarsa.
''Sajan din ya zargi likitar da rashin neman izinin sa kafin duba lafiyar matarsa wanda a al'adarsu, hakan laifi ne."

Kara karanta wannan

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

Ahmed ya ce matar bawai kankanuwar yarinya ba ce, ya kuma kara da cewa akwai kawarta a tare da ita kafin gudanar da gwajin.

Ya bayyana cewa sajan din ya jiwa likitar ciwo kafin a kwace shi a hannun sa.

Ya kuma bayyana cewa tuni wanda ake zargi ya shiga hannu inda yake tsare a hannun yan sanda.

Ya kara da cewa:

''Abin takaici ne ace haka tana faruwa da mu. Aikin mu da yawa, ga kuma sauran matsalolin yau da kullum, ciki har da wahalar naira da karancin mai.
''Muna zuwa aiki tun 7:00 na safe kuma sai dare zamu tafi gida, mutanen da muke ceton rayuwarsu suna zagi da farmakar likitocin mu.
''Mun yi duk mai yiwuwa don wayar da kan mutane da hanyar kafafen sadarwa, banoni da shirye shirye da dana da ke gargadin mutane da su daina cin zarafin likitoci.
''Irin wannan ya faru a asibitin koyarwa na jami'ar Illorin. Idan mutane suna daukar doka a hannu, ba za mu bar likitocin mu su mutu ba.''

Kara karanta wannan

Assha: Ana jibi zabe, motocin jigilar kayan aikin zabe sun lalace a hanya a wata jiha

Ahmed ya ce ba sa ganin laifin gwamnatin jihar amma suna kare lafiyar ma'aikatansu.

Daraktan Asibitin ya tabbatar da afkuwar lamarin

Da ya ke bayani akan batun, babban daraktan asibitin, Dr Bola Abdulkadir, ya ce hukumar asibitin tana sane da lamarin kuma tana yin duk mai yiwuwa don shawo kan lamarin.

Abdulkadir ya bada tabbacin gwamnatin jihar tana sane da irin hare-haren tana kuma duk yiwuwa don tabbatar da kare lafiyar likitocin.

''Muna tabbatar musu cewa hukumar asibiti da gwamnatin Jiha suna iya kokari don kare faruwar haka nan gaba.
''Manyan likitoci za su ci gaba da kula da majinyata, to akwai hanyoyin cigaba da bada kulawa,'' ya bada tabbaci.

Daraktan ya kuma yaba da kokari da sadaukarwar ma'aikatan lafiya wajen ceton rayuwar al'umma a asibitin.

Wani ya sheke abokinsa ya birne gawarsa saboda kudi a Abuja

Yan sanda sun kama wani mutum dan shekara 63 mazaunin Abuja, Taiwo Ojo, kan zarginsa da halaka abokinsa mai suna Philip Kura.

Kara karanta wannan

An Tsaka Da Karancin Naira, An Kama Wani Da Tsabar Sabbin Kudi N250,000 Na Bogi

Ojo ya rafka wa Philip cebur ne a kansa yayinda suke cacar baki kan wani kudi kuma ya janye gawar sa ya boye a cikin wani dan karamin daji, kafin daga baya ya birne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel