Yadda Wani Mutum A Abuja Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Birne Gawarsa Saboda Kudi

Yadda Wani Mutum A Abuja Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Birne Gawarsa Saboda Kudi

  • Yan sanda sun kama wani mutum, Taiwo Ojo, dan shekara 63 a Abuja kan zargin kashe abokin aikinsa
  • Rahotanni daga majiyoyin binciken sirri sun ce wanda ake zargin ya halaka abokin aikinsa ne kan batun wani kudi da ya shiga tsakaninsu
  • A halin yanzu wanda ake zargin yana hannun jami'an yan sanda kuma ana zurfafa bincike

FCT, Abuja - Wani mutum mazaunin birnin tarayya Abuja dan shekara 63 da ke sana'ar panel beater, Taiwo Ojo ya shiga hannun yan sanda kan kashe abokin aikinsa.

An kama Ojo ne saboda zarginsa da kashe abokin aikinsa mai suna Philip Kura, ya kona gawarsa ya kuma birne shi a wani kabari mara zurfi a Bwari, da ke birnin tarayya Abuja, rahoton The Punch.

Yan sandan Najeriya
Yadda Wani Mutum A Abuja Ya Kashe Abokin Aikinsa Ya Birne Gawarsa Saboda Kudi. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Ta tabo inda yake so: Amarya ta shafa kirjin ango a wurin biki, ya cika mata jaka da daloli

Daily Post ta rahoto cewa Ojo ya halaka abokin aikinsa ne saboda jayayya da suka yi kan wani kudi a ranar 23 ga watan Disamba, kamar yadda wata majiya na bayanin sirri ta bayyana.

Majiyar ta ce:

"Ojo da Kura sun sunyi rikici a shagonsa a ranar 23 ga watan Disamba. Ojo ya bugi wanda abin ya faru da shi da shebur a kansa kuma ya fadi ya mutu.
"Ya janye gawarsa ya boye karkashin bishiyoyin ayaba da ke kusa sannan daga bisani ya kona tare da birne gawar marigayin a wani kabari mara zurfi."

Rundunar yan sandan na cigaba da zurfafa bincike kuma idan an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu don yin shari'a.

Yan sanda sun kama wani ya dura wa kabarin wata ashar a faifan bidiyo

A wani rahoton, yan sandan jihar Kano sun cika hannunsu da wani Abdullahi Yar Dubu, bayan fitar wani faifan bidiyo da ya nuna shi yana dura ashariya a kabarin mahaifiyar abokinsa.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kama Yahoo Boys Da Suka Sace Abokin Aikinsu Don Ya Hana Su Kasonsu Cikin N22m Na Zamba

Kakakin yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa an cafke Yar Dubu kuma an kai shi hedkwatar yan sanda inda ake masa tambayoyi da zurfafa bincike.

Zuwa yanzu ba a sanar da abin da ya saka matashin ya tafi ya yi wannan abin da bai dace ba, yayin da galibin mutane a shafukan soshiyal midiya suna ta yin Allah wadai da abin da ya aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel