Babbar Magana Yayin da Motocin da Suka Dauko Kayan Aikin Zabe Suka Makale a Jihar Kuros Riba

Babbar Magana Yayin da Motocin da Suka Dauko Kayan Aikin Zabe Suka Makale a Jihar Kuros Riba

  • Yayin da ake ci gaba da jiran cikar ranar da za a yi zaben shugaban kasa, motocin daukar kayan aikin zabe sun makale a wani garin
  • Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da motocin ke daukar kaya zuwa Arewacin jihar Kuros Riba a Kudancin Najeriya
  • A ranar Asabar 25 ga watan Faburairu ne za a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, ‘yan talara da masu ruwa da tsaki a zaben suna ta shiri

Jihar Kuros Riba - A wani bidiyon da ya yadu a ranar Alhamis, an ga yadda wasu motocin da suka dauko kayan aikin zaben na hukumar INEC suka samu tsaiko a hanya.

Jaridar Punch ta bayyana cewa, wannan lamari ya haifar da cunkoson ababen hawa da ta kai ga sauyawa mutane hanyar bi a yankin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Yadda Mafarauci Ya Zakulo Katukan Zabe Na PVC a wani Dajin jihar Anambra Yan Kwanaki Kafin Zabe

Idan baku manta ba, a ranar 25 ga watan Faburairun 2023 za a yi zaben shugaban kasa a Najeriya, ana ci gaba da kai muhimman kayan aikin zaben zuwa jihohi da kananan hukumomi.

Yadda motar daukar kayan aikin zabe ta lalace a jihar Akwa Ibom
Motocin da suka dauke kayan aikin zabe sun lalace a hanya | Hoto: Punch Newspaper
Asali: Facebook

An samu tsaiko, kayan aikin zabe ya makale

A bidiyon da aka yada, an ji wani mutum a ciki yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wannan shine bidiyon kayan aikin zaben da aka dauka za a kai Arewacin jihar Kuros Riba. Wasu daga cikin manyan motocin sun lalace don haka kowa ya tsaya tsak, babu abin da yake tafiya, kusa da mahadar Sojoji.
“Dukkan kayan aikin INEC sun makale ga kuma mutane suna gujewa cunkoso suna bin hannu daya na titin. Daya hannun titin da ke dauke lalatattun motocin kayan aikin INEC ya toshe.”

Hukumar zabe dai ta bayyana cewa, ta gama shirin daram don tunkarar wannan zaben na bana, kuma ta ce bata hango wani tsaiko da zai faru.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: An kai muhimman kayan aikin zabe shugaban kasa jihar Gombe, INEC ta magantu

An fara raba muhimman kayan aikin zabe a jihar Gombe

A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta fito kayayyakin da za a yi amfani dasu wajen zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a bana a jihar Gombe.

Hukumar zaben ta bayyana cewa, komai ya kankama, kuma za a kai kayayyakin kananan hukumomin da za a yi zaben.

An ruwaito cewa, hukumar ta adana kayayyakin aikin zaben ne reshen Babban Bankin Najeriya (CBN) na Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel