Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Bankawa Ofishin INEC Wuta a Jihar Kano

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Daba Suka Bankawa Ofishin INEC Wuta a Jihar Kano

  • Wasu 'yan daba sun bankawa ofishin hukumar zabe ta INEC wuta a jihar Kano, sun hallaka mutane hudu inji majiyoyi
  • Hakazalika, rahoto ya bayyana cewa, an jikkata wasu mutane da basu ji ba basu gani ba a lokacin da rikicin ya barke
  • Ya zuwa yanzu, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce bata san ko an rasa rayuka a rikicin ba

Takai, jihar Kano - Wasu fusatattun mutane sun yi kokarin kone ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne lokacin da aka tsamu tasgaro tsakanin mabiya jam’iyyun siyasa a hedkwatar INEC da ke Takai da safiyar ranar Lahadi 26 Faburairu, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bola Tinubu Ya Lashe Kananan Hukumomi 10 Daga Cikin 20 a Jihar Ogun

An farmaki ofishin INEC a Kano
Yadda aka saka wa ofishin INEC wuta a Kano | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewar shaidan:

“An cinna wutar ne ta bayan ginin amma an kashe ta kafin ta yi barna mai yawa kuma jami’an tsaro sun watsa taron jama’a.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Sai dai, wasu mutane sun samu raunuka da kitimurmurar da aka fara da farko; amma an dauke su zuwa asibiti domin yi musu jinya yayin da aka kashe mutum hudu.”

A fadin wani shaidan gani da ido na daban, lamarin ya barke ne a lokacin da aka fara tattara sakamakon zaben karamar hukumar, cewar rahoton BBC Hausa.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa, an bankawa dakin janarentan ofishin na INEC ne, amma an gaggauta kashe cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

Daga sintirin sa ido: 'Yan daba sun yi kaca-kaca da tawagar EFCC a filin zabe a Abuja

A cewarsa:

“Ta dakin janareta ne suka banka wutar. Cikin gaggawa aka kashe wutar kuma jami’an tsaro sun mamaye wurin.”

Sai dai, Kiyawa ya ce rundunar bata samu labarin rasa rayuka da aka yi a hedkwatar ba.

An kone akwatunan zabe a Edo

A wani labarin, kun ji yadda wasu ‘yan daba suka kone akwatunan zabe a jihar Edo biyo bayan jefa kuri’u a wata rumfar jihar.

Rahoton da muke samu daga jihar ya bayyana cewa, an kada kuri’u, sai kawai wasu ‘yan daba suka farmaki jama’a suka kone komai.

An samu wurare daban-daban a Najeriya da aka farmaki masu kada kuri’u da ma’aikatan zabe a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel