Tinubu Ya Shigar da Kara Domin Hana Jam’iyyar Labour da PDP Dakatar da Tattara Sakamakon Zabe
- Bola Ahmad Tinubu ya tafim kotu don dakatar da yunkurin 'yan PDP da LP wajen tabbatar da an tsaya da batun tattara sakamakon zaben bana
- Tinubu da Shettima sun ce dakatar da tattara sakamakon zabe zai jawo asara, don haka a ci gaba don gano wanda ya ci zabe
- A gege guda, Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Borno, ya fi Atiku da kur'u sama da 60,000
Jihar Kano - Bola Ahmad Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ya shigar da kara hukumar zabe ta INEC da Action Alliance don dakatar da jam’iyyar Labour da PDP daga yunkurin hana ci gaba da tattara sakamakon zaben bana.
Tinubu, wanda shine dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ce sam ba zai bari a dakatar da tattara sakamakon da ya hango zai kaishi Villa ba a zaben na bana.
Idan baku manta ba, an yi zaben shugaban kasa a Najeriya a ranar 25 ga watan Faburairu, kuma Tinubu ke kan gaba a yawan kuri’u.

Source: Facebook
Karar da Tinubu ya shigar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin karar da ya shigar a Kano mai lamba FHC/KN/CS/43/2023, an ambaci INEC da Action Alliance a matsayin wadanda ake kara, Daily Trust ta ruwaito.
Hakazalika, abokin takararsa, Kashim Shettima ne mutum na biyu bayan shi a wadanda ke shigar da kara a gaban kotun tarayyar da ke Kano.
A karar, Tinubu da Shettima sun nemi kotu da ta hana kawo tsaiko ko dakatar da tattara sakamakon zaben da tuni an fara nisa.
A cewarsu, dakatar da tattara sakamakon zai jawo asara mai yawa ga wadanda suka shigar da kara matukar aka bi ta su PDP da LP aka dakatar, Punch ta ruwaito.
A halin da ake ciki, har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, kuma alamu sun nuna Tinubu ya fi yawan kuri’u a jihohin da aka sanar.

Kara karanta wannan
2023: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Baturen Zabe Na Jihar Rivers Ya Dakatar Da Tattara Sakamakon Zabe
Tinubu ya lashe Borno
A wani labarin, kunji yadda Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Ya samu kuri'u sama da 250,000, inda ya ba Atiku na jam'iyyar APC kuri'u sama da 60,000 a zaben bana a jihar.
Asali: Legit.ng
