Dan Takarar APC Tinubu Ya Ba Atiku da Obi Shawari, Ya Ce Su Rungumi Kaddara

Dan Takarar APC Tinubu Ya Ba Atiku da Obi Shawari, Ya Ce Su Rungumi Kaddara

  • Dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu ya bayyanawa ‘yan takarar shugaban kasa da su daina tada hankali
  • Tinubu ya ce ya kamata Atiku da Obi su yi koyi da halin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben bana
  • Ya kuma yi tsokaci ga yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nemi a soke sakamakon zaben bana

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya shawarci dan takarar PDP, Atiku Abubakar da na LP Peter Obi da su rungumi kaddara irin na tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

Tinubu ya bayyana cewa, matukar aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a kasar, to kamata ya yi su saduda, sun rumgumi kaddara.

Tinubu ya bayyana wannan batun ne ta bakin hadiminsa a fannin yada labarai, Mr. Dele Alake, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: INEC Ta Sanar da Sakamakon Jihar Zamfara, Atiku da Kwankwaso Sun Sha Kashi

Bola Tinubu ya shawari Atiku da Obi su rungumi kaddara
Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC | Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

A jawabansa, Tinubu ya gargadi PDP da LP da su guji dago matakar soke sakamakon zabe, inda yace hakan daidai ba zai yiwu ba, domin kamar ciki ne da ba za a iya zubar dashi ba bayan ya girma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya zo da tsallen badahu

A bangare guda, Tinubu ya zargi tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanji da kokarin jefa kasar dimokradiyya irin Najeriya cikin hadari ta hanyar kira ga soke zaben bana na wasu sassan kasar.

A wani taron manema labarai a Abuja, Alake ya ce, maganar Obasanjo ba ta da ma’ana, kuma ya yi ta ne ta hanyar da LP da PDP suka kitsa masa.

A cewarsa, jam’iyyun biyu sun hango faduwa ne a zaben bana, saboda haka suke son a tarnake komai a kasar ta hanyar yada karya, The Street Journal ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Obasanjo Ya Nemi a Soke Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya, kuma Bola Tinubu ne ke kan gaba a zaben na bana.

Peter Obi ne ya ci zabe a jihar Legas ta Tinubu

A wani labarin, kunji yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya lallasa Bola Ahmad Tinubu da Atiku Abubakar a jihar Legas.

A rahotannin da aka samu daga wurin tattara sakamakon zaben shugaban kasa na bana, an ce Obi ne ya samu mafi yawan kuri’un Legas, inda yake ba Tinubu kusan kuri’u 10,000.

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya, ‘yan takara na ci gaba da bayyana matsayarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel