Yan Daba Sun Tafi Gidan Wani Dan Gani Kashe Nin Tinubu, Sun Lakada Wa Mahaifiyarsa Duka, Sun Kona Motarsa

Yan Daba Sun Tafi Gidan Wani Dan Gani Kashe Nin Tinubu, Sun Lakada Wa Mahaifiyarsa Duka, Sun Kona Motarsa

  • Wasu yan tada kayar baya sun kai hari gidan wani magoyin bayan APC tare da lalata kadarori da dama a Jihar Ogun
  • Rahotanni sun bayyana yadda suka yi rauni ga mai gadi tare da dukan mahaifiyar mutumin lokacin da suke kai harin
  • Har zuwa lokacin kammala wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin yan sandan Jihar ba dangane da lamarin

Ogun - Wasu yan tada kayar baya da ba a san ko su wanene ba sun kai hari gidan wani mutum Michael Yomi Agboola, wani dan gani kashe nin jam'iyyar APC a Itele-Ota da ke Jihar Ogun.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yan tada kayar bayan sun dira a gidan mai lamba 12, Titin Agboola, Iteja-Ota, da safiyar Lahadi biyo bayan nasarar dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu a yankin.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama DSS Na Bogi Yayin Da Ake Zabe A Osun

Ogun Map
Taswirar Jihar Ogun. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Menene ainihin abin da ya faru?

An fasa gidan da harsashi, kuma dattijuwar da ke gidan a lokacin harin wadda ita ce mahaifiyar Agboola ta sha duka inda har taji rauni a hannun yan tada kayar bayan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa an kuma yiwa mai gadin gidan mummunan rauni kuma a yanzu haka yana sashen bada kulawa ta musamman a asibiti.

Wani da ya shaidar lamarin ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan tada kayar bayan da za su kai 20 sun yi ta harbi ba kakkautawa a gidan tare da alwashin sai sun fito da Agboola duk inda ya boya.

Shaidar gani da idon ya ce yan tada kayar bayan na ta ihun, ''Meyasa zai goyi bayan APC? Sai mun kaiwa duk magoya bayan Jagaban hari anan unguwar. Nemansa muke, dole mu gan shi.''

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

Da ya ke bayani daga maboyarsa, Agboola cikin muryar kuka ya ce harin ya bata masa rai kuma yayi mamaki.

Ya bayyana cewa an lalata masa kadarorin miliyoyin dukiya, kuma an yiwa mahaifiyarsa rauni a hari.

Ya roki yan sanda da sauran jami'an tsaro da su tabbatar an kama masu laifin.

Agboola ya kara da cewa:

'Na ji bakin cikin harin da aka kai gidana. Me yasa za a kawo min hari kawai saboda ina goyon bayan dan takarata a APC? An daki mahaifiyata. An lalata min motata da ke ajiye a gidan, shima mai gadi anyi masa rauni.
''Sun yi min haka ne kawai saboda ina goyon bayan Tinubu. Sun lalata min gida kuma sun yi barazanar za su illata ni idan na shiga hannun su.''

Ba samu nasarar yunkurin jin ta bakin hukumar yan sandan Jihar Ogun kan lamarin ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel