Yan Sanda Sun Kama DSS Na Bogi Yayin Da Ake Zabe A Osun

Yan Sanda Sun Kama DSS Na Bogi Yayin Da Ake Zabe A Osun

  • Wasu mutane sun yi sojan gona tare da tunkarar yan sanda don neman hadin kai wajen aikin zabe a jihar Osun
  • Mutanen biyu sun yi sojan gona a matsayin jami'an hukumar DSS kafin fara zabe a Jihar Osun
  • Rundunar yan sandan Jihar Osun, ta tabbatar da faruwar lamarin tare ba bayyana cewa wanda ake zargin suna hannun DSS

Jihar Osun - An kama mutum biyu da zargin sojan gona ga hukumar tsaron farin kaya, DSS, a Illa Orangun, Jihar Osun kafin fara kada kuri'a ranar Asabar, Vanguard ta rahoto.

An ruwaito cewa jami'an bogin sun yi shiga irin ta jami'an DSS, suka tunkari yan sanda don neman hadin kai wajen gudanar da aikin zabe.

Taswirar Jihar Osun
An kama jami'an DSS na bogi a wurin zabe a Osun. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A wani bidiyo da yake yawo wanda ya nuna lokacin da aka kama su, jami'an sojan gonar sun ce suna aiki ne ba wani kamfanin tsaro mai zaman kansa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun bada tabbacin cewa mai gidan su da aka sani da Janar Gerard Olatunbosun shi ya turo su yankin don gudanar da aikin zabe.

Sun bayayyana sunan su a matsayin Olarewaju Funiran da Sodiq Olayemi.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar yan sanda ta Jihar Osun, Yemisisi Opalola ya ce

''An kama mutum biyu da yin sojan gona ga hukumar DSS kafin fara zabe ranar Asabar. Su na hannun hukumar ta DSS.''

An sha mamaki yayin da aka kama malamin jami'ar Najeriya dauke da tsabar kudi N306,700 a wurin zabe

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, sun kama wasu mutane da ake zargi da siyan kuri'a a jihar Benue.

Kara karanta wannan

Hukumar Yan Sanda Ta Yi Karin Haske Kan Harin Da Boko Haram Suka Kaiwa Masu Zabe a Borno

Sanarwar da hukumar EFCC ta fitar ya ce an kama Dakta Cletus Tyokyya, malami a Jami'ar Sarwuan Tarka (tsohuwar Jami'ar Noma) da tsabar kudi naira N306,700 a cikin jaka a motarsa.

An damke shi ne yayin da ya taho wata rumfar zabe da ba tasa ba kuma da ya lura jami'an tsaro sun tunkaro kansa ya yi kokarin ya tsere amma bai yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel