Ana Gobe Zabe, An Kama Wani Mutum Da Maƙuden Miliyoyin Naira A Mota Zai Kai Wa Ɗan Siyasa A Gombe

Ana Gobe Zabe, An Kama Wani Mutum Da Maƙuden Miliyoyin Naira A Mota Zai Kai Wa Ɗan Siyasa A Gombe

  • An kama wani mutum dauke da takardun naira cikin jaka ta 'Ghana must go' a mota a jihar Bauchi
  • Mutumin mai suna Hassan Ahmed ya bayyana cewa zai kai wa wani dan siyasa ne kudin a jihar Gombe
  • Mai magana da yawun hukumar ICPC a Bauchi, Ogugu, ya ce suna yi wa wanda ake zargin tambayoyi don zurfafa bincike

Jihar Bauchi - Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta kama wani Hassan Ahmed dauke da tsabar kudi naira miliyan 2 na sabbi da tsaffin naira a yayin da ake fama da karancin kudi a kasar, rahoton The Punch.

Dakarun 33 Artillery Brigade da aka tura Alkaleri a jihar Bauchi ne suka kama shi a ranar Juma'a 24 ga watan Fabrairu suka mika shi ga ofishin hukumar yaki da rashawar a Bauchi.

Kara karanta wannan

Kamfen Kwankwaso: An kame 'yan daba 55, an kone wani adadi na motoci a Kano

Wanda ake zargi
Jami'in ICPC da wanda aka kama da tsabar takardun naira miliyan biyu a Bauchi. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren ranar Juma'a.

Ogugua ya ce:

"Ahmad na dauke da tsabar kudi N900,000 na sabbin naira da N1.1 miliyan na tsaffin naira kuma yana dauke da kudin ne cikin wata mota kirar Hilux mai bakin launi mai lamba JMA 85 AZ.
"Kudin da aka saka su cikin jaka ta 'Ghana Must Go, sun hada da kunshin N1,000 na N600,000, kunshi shida na sabbin N500 na N300,000, da tsaffin naira dari biyu na N1.1 miliyan."

Ogugua ya kara da cewa hukumar ta riga ta fara bincike, a yayin da wanda ake zargin ya bayyana cewa yana hanyar kai wa wani dan siyasa ne kudin a Jihar Gombe.

Ana fama da karancin takardun naira, an kama wani mutum da tsabar kudi na N250,000 na jabu a Ekiti

Kara karanta wannan

Kano: DSS Ta Gano Bindigu, Takubba Da Sauran Muggan Makamai A Ofishin Kamfen

A wani rahoton kun ji cewa jami'ar hukumar tsaro na Amotekun a jihar Ekiti sun kama wani Celestine da takardun naira na bogi da suka kai N250,000.

Wanda ake zargin ya fada wa jami'an tsaron cewa wani mutum ne ya bashi takardun nairan ba tare da ya san cewa na bogi bane.

Birgediya Janar Joe Komolafe (mai murabus), babban kwamandan Amotekun ya ce an cafke wanda ake zargin ne a garin Omuo Ekiti a karamar hukumar Ekiti ta Gabas yana kashe takardun N1000 na jabu a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel