An Kone Motoci Shida, an Kama ’Yan Ban Siyasa 55 a Lokacin Kamfen Din Kwankwaso Na Kano

An Kone Motoci Shida, an Kama ’Yan Ban Siyasa 55 a Lokacin Kamfen Din Kwankwaso Na Kano

  • An samu tsaiko a jihar Kano yayin da wasu tsagerun ‘yan daba suka tada hankalin jama’a ba tare da wani dalili ba
  • An samu tashin hankali, an kone motoci har shida, inji hukumar tsaro ta NSCDC a yau Alhamis 23 Faburairu, 2023
  • An kuma kame ‘yan daba 55 da ake zargin su suka tada hankali tare da yin kone-kone a jihar da ke Arewa maso Yamma

Jihar Kano - Rahoton da muke samu ya bayyana cew,a akalla motoci shida ne aka kone a jihar Kano biyo bayan hargitsin da aka samu tsakanin mabiya NNPP da wasu jam’iyyu.

Hakazalika, an ce an kama mutum 55 da ake zargi da tada hankali a lokacin kamfen din dan takarar shugaban kas ana NNPP, Rabiu Kwankwaso, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kamfen din karshe: 'Yan daba sun farmaki magoya bayan Kwankwaso, sun kone motoci a Kano

Wannan na zuwa ne daga bakin kakakin rundunar hukumar tsaro ta NSCDC, Mr. Ibrahim Idris Abdullahi a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis.

An kone motoci 6, an kama 'yan daba 55 a Kano
Yadda aka kone motoci a Kano ranar kamfen Kwankwaso | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, an kama tsagerun ‘yan daban ne a kan titin Zaria dauke da muggan makamai a ranar kamfen Kwankwaso.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

A cewarsa, tsakanin karfe 3 na yamma a ranar Alhamis 23 Faburairu, 2023, an sanar da hukumar yadda rikicin ‘yan daba ya barke tsakanin jam’iyyun siyasa, rahoton The Nation.

Ya bayyana cewa:

“Cikin gaggawa muka tura mutanenmu wurin da lamarin ya faru, a can, muka kama tsagerun ‘yan daba dauke da makamai.”

Mr. Abdullahi ya kuma kara da cewa, ‘yan daban da aka kama ana zargin su suka tada kura a garin, duk da cewa ana ci gaba da bincike don gano bakin zaren.

Kara karanta wannan

Kalamansa Sun Jawo Masa, Za a Shiga Zabe, Kotu ta Daure ‘Dan Takara a Kurkuku

Kamfen Kwankwaso da APC ya zo a rana daya

Idan baku manta ba, dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a yau ya rufe taron gangaminsa na kamfen gabanin zaben shugaban kasa.

Har ila yau, a ranar dai jam’iyyar APC ma ta bayyana yin kamfen karshe na shekarar yayin da ake tunkarar ranar zabe ta Asabar.

Sai dai, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya shawarci jam’iyyun siyasan biyu da su dage kamfen din nasu kawai saboda gudun rikici.

A tun farko, mun kawo muku rahoton yadda aka tare ‘yan Kwankwasiyya tare da farmakarsu a hanyar Zaria a kwaryar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel