Jerin Malaman Addini 5 da Suka Shiga Siyasa, Suke Neman Takara a Zaben 2023

Jerin Malaman Addini 5 da Suka Shiga Siyasa, Suke Neman Takara a Zaben 2023

  • Nan da ‘yan kwanaki za a fara zaben gwamnoni a jihohin Najeriya guda ashirin da takwas
  • A cikin wadanda suka fito takara na mukamai dabam-dabam, akwai wadanda malaman addini ne
  • Malamai da Fastoci sun yi tsamo-tsamo a siyasar 2023, su na neman kujerar Gwamnoni a wasu Jihohi

A ranar Asabar, za'a gudanar da zaben gwamnonin Najeriya kuma akwai malaman da suke burin mukamin Gwamnati a zaben nan:

1. Sheikh Ibrahim Khaleel

Sheikh Ibrahim Khaleel yana cikin masu neman takarar gwamna a Kano, shi ne shugaban majalisar malaman jihar, ya samu takara ne a jam’iyyar ADC.

Ibrahim Khalil ya nemi ya zama ‘dan takarar Gwamnan Kano a karkashin ANPP tun zaben 2011.

2. Fasto zai tada hankalin PDP

A Benuwai, Rev. Fr. Hycainth Iormem Alia shi ne ‘dan takaran Gwamna a karkashin jam’iyyar APC mai adawa a jihar zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rabaren Hycainth Alia shi ne limanin cocin katolika na Saint Thomas Parish da ke Makurdi.

Isaac Idahosa
Bishof Isaac Idahosa a Oyo Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

3. Fasto Umo Eno

Umo Eno shi ne wanda Mai girma Gwamna Udom Emmanuel ya tsaida a matsayin wanda zai gaje shi a gidan gwamnatin Akwa Ibom a watan Mayun 2023.

‘Dan takaran na PDP ya yi kwamishina a gwamnati mai-ci, kuma Fasto ne da ake ganin kimarsa.

4. Za a buga da Fastoci a Kuros Riba

Fasto Usani Usani wanda ya rike Ministan Neja-Delta a gwamnatin Muhammadu Buhari yana neman takarar Gwamnan Kuros Riba a jam’iyyar adawa ta PRP.

Rahoton ya ce tsohon shugaban jam’iyyar ta APC ya kan hay mimbarin Liberty Church jifa-jifa.

A zaben shekarar nan akwai wasu Fastoci a jihar Kuros Ribas da ke neman takara.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Dace A Sani Game Da Umar Namadi, Dan Takarar Gwamnan APC a Jigawa

5. Ogar Osim

Wani Fasto da yake harin kujerar Gwamna a Kuros Riba shi ne Ogar Osim. Matashin da ke takara a jam’iyyar LP yana aiki a cocin Patriarch Christ Shepherd.

Dage zaben gwamna

Hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta bayyana cewa ranar Talata, 14 ga watan Maris 2023 zata kammala aikin da take yi kan na'urar tantance masu zabe ta BVAS.

Hukumar ta bukaci a dage zaben ne saboda wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel