Sauya Naira: Mutane Suna Cikin Yunwa Kuma Sun Fusata, Sultan

Sauya Naira: Mutane Suna Cikin Yunwa Kuma Sun Fusata, Sultan

  • Sultan, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga mahukunta su gaggauta kawo karshen wahalar karancin naira
  • Mai Alfarma Sarkin Musulumin ya ce sabon tsarin ya jefa mutane cikin yunwa kuma tuni suka fara kaiwa bango
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da ƙuncin rashin naira a hannu ke kara tsananta a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya ce tsarin sauya fasalin naira wanda ya haddasa ƙarancin takardun kuɗi ya jefa mutane cikin ƙunci da takaici.

Sultan ya bayyana haka ne ranar Litinin a wurin taron "Farfaɗo da kiyon dabbobi da magance rikice-rikice masu alaƙa," kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Sarkin Musulmi.
Sauya Naira: Mutane Suna Cikin Yunwa Kuma Sun Fusata, Sultan Hoto: Thecable
Asali: UGC

Sarkin Musulmin ya ce ya zama wajibi hukumomi masu ruwa da tsaki kan sabon tsarin su yi duk me yuwuwa wajen sanyaya zuƙatan mutane da wahalhalun da suka shiga.

Kara karanta wannan

Shin CBN Ya Kara Wa'adin Amfani da Tsoffin Kuɗi? Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani a Halin Yanzu

Duk da Kotun Koli ta umarci FG ta jinkirta haramta amfani da tsoffin naira da ta tsara ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023, har yanzun ana fama da ƙarancin naira a hannu a sassan ƙasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai Alfarma Sarkin Musulmai ya ce:

"Mutane suna fama da yunwa, shin akwai kuɗi? Babu tsabar takardun naira. Mutane sun fusata kuma ga yunwa na damunsu, bari mu ga yadda zamu yayyafa wa yanayin nan ruwan sanyi."

Akwai bukatar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya - Sultan

Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ƙara da cewa ya kamata zaman tattaunawa irin wannan ya lalubo hanyoyi magance rikicin manoma da makiyaya a ƙasar nan kuma a aiwatar tun daga tushe.

A ruwayar Sahara Reporters, Sultan ya ci gaba da cewa:

"Ya kamata mu jingine siyasa a gefe, mu baiwa ci gaba muhimmanci musamman a kan gama garin mutum. Bayan turancin farfesoshi a aji, ta ya ci gaba zai kai ga talakan manomi ko Fulani wanda bai san komai ba sai kiwo."

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: CBN Ya Zo Da Sabon Shiri Mai Kyau Na Kawo Karshen Karancin Sabbin Kuɗi a Najeriya

"Na je jihar Benuwai a matsayin Sultan sau biyu muna zama da gwamnoni da Sarakuna mu tattauna hanyoyin samun zaman lafiya a jihar. Daga karshe za'a samu shawarwari amma sai mu watsar."
"Ya kamata wannan taron ya banbanta da sauran, mu nemo hanyoyin kuma mu aiwatar da su yanzu ba sai wani lokaci ba."

Babban banki CBN na shirin raba sabbin kudi N1trn ga bankuna

A wani labarin kuma CBN ya kammala shirin yaye ƙuncin da 'yan Najeriya suka shiga sanadin sabon tsarin sauya fasalin naira

Rahoto daga wani mai faɗa a ji a CBN ya nuna cewa babban bankin ya kammala shirin raba sabbin takardun da aka buga kusan Tiriliyan ɗaya a sassan Najeriya.

Mutane sun shiga kunci tun bayan da CBN ya kawo tsarin sauya kuɗi ba tare da wadata su da sabbin da aka canja ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel