Babban banki CBN na shirin raba sabbin kudi N1trn ga bankuna

Babban banki CBN na shirin raba sabbin kudi N1trn ga bankuna

  • CBN ya kammala duk wasu shirye-shiryen raba kusan Tiriliyan ɗaya ga bankunan kasuwanci domin rage raɗaɗin da mutane ke ciki
  • Wani mamban majalisar gudanarwa ta CBN da ya nemi a sakaya sunansa, shi ne ya bayyana shirin babban bankin
  • Fito da makudan kuɗi irin wannan na sabbin naira a halin yanzu wani yunkuri ne na wucewa da tunanin wasu gwamnoni a Najeriya

FCT Abuja - Alamu sun nuna babban bankin Najeriya (CBN) ka iya sake antayo ƙarin takardun sabbin kuɗi zuwa hannun al'umma ta bankunan kasuwanci yau Litinin, 13 ga watan Fabrairu, 2023.

A rahoton da jaridar The Nation ta haɗa, kusan biliyan N500bn na sabbin takardun da aka sauya wa fasali ne ake hada-hada da su tun daga watan Disamba, 2022.

Gwamnan CBN da na Kaduna.
Babban banki CBN na shirin raba sabbin kudi N1trn ga bankuna Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Twitter

Yaushe sabbin naira zasu wadata?

Kara karanta wannan

Gaskiya 3 Da Ya Kamata Ku Sani Game da Matsayin Tsoffi Da Sabbin Naira a Yanzu

Wani mamban majalisar gudanarwan CBN, wanda ya yi jawabi da sharaɗin boye bayanansa, yace bankin zai rabawa bankuna kusan Tiriliyna ɗaya (N1trn) ranar Litinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwan jami'in babban bankin ta ce:

"CBN zai yi duk abinda ake bukata domin tabbatar da ya kawar da ƙuncin rayuwar da 'yan Najeriya suka tsinci kansu."
"Saboda haka, za'a rabawa bankunan kasuwancin ƙarin sabbin takardun naira daga ranar Litinin domin mutane su samu damar cirewa."

Wannan sabon motsi da babban bankin ya yi ka iya zarce tunanin wasu gwamnoni a Najeriya, waɗanda suka yi ikirarin gwamnan CBN na da wata boyayyar manufa.

A cewar gwamnonin ciki harda na Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, Godwin Emefiele, na da wata manufa a ɓoye saboda bai tashi kawo tsarin ba sai a kakar zaɓe.

This Day tace Akalla gwamnatocin jihohi Bakwai ne suka shiga Kotu suna kalubalantar sabon tsarin da FG ta kawo, sun ƙara da cewa lamarin ya jefa da yawan yan Najeriya cikin ƙunci.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: CBN Ya Fitar Da Sabuwar Sanarwa Kan Karancin Naira, Ya Musanta Barazanar Rufe Bankuna

Babban Banki CBN Ya Musanta Barazanar Rufe Wasu Bankuna

A wani labarin kuma CBN ya musanta barazanar cewa yana shirin rufe wasu bankuna sakamakon karancin sabbin naira

A wata sabuwar sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan sashin hulɗa da jama'a, CBN ya ce babu wannan shirin ko kaɗan.

CBN ya tabbatarwa yan Najeriya cewa zai yi duk mai yuwuwa don ya tsamo su daga wahalhalun kuncin rayuwar da suka shiga sanadin canja naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel