Shin CBN Ya Kara Wa'adin Amfani da Tsoffin Kuɗi? Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani

Shin CBN Ya Kara Wa'adin Amfani da Tsoffin Kuɗi? Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani

  • Karancin sabbin takardun naira ya jefa da yawan yan Najeriya cikin wahala yayin da CBN ya yi gum kan halascin ci gaba da amfanu da tsoffin kuɗi
  • Wasu 'yan kasuwa a Najeriya sun fara ƙin karban tsohon kuɗi duk da hukuncin Kotun ƙoli na dakatar da FG daga aiwatar da tsarin har sai 15 ga watan Fabrairu
  • Matakin da Kotun ta ɗauka ya haddasa kace-nace da ruɗani tsakanin masu kiran a ƙara wa'adi da masu goyon bayan tsarin CBN

Har yanzun da yawan 'yan Najeriya basu san takamaiman halin da ake ciki ba kan batun wa'adin daina amfanin da tsoffin takardun naira duk da Kotun ƙoli ta umarci FG ta jinkirta zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, 2023.

Jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara ne suka garzaya Kotun koli, suka roki ta taka wa FG da CBN burki a yunkurinsu na haramta amfani tsoffin takardun N200, N500, da N1000, a cewar rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Tsoffin Kudi: Gwamna Masari Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Bankuna Da Yan Kasuwa a Jihar Katsina

Gwamnan CBN da Buhari.
Shin CBN Ya Kara Wa'adin Amfani da Tsoffin Kuɗi? Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Hoto: CBN
Asali: Facebook

Wane mataki CBN ya ɗauka bayan umarnin Kotun Koli?

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton dake cewa Kotun koli ta amince da bukatar cikin shari'a, inda ta dakatar da gwamnatin tarayya daga ci gaba da aiwatar da shirinta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai wannan mataki na Kotun koli ya haddasa ruɗani da cece-kuce a tsakanin mutanen dake fatan mahukunta su ƙara wa'adin da kuma masu son CBN ya aiwatar da tsarinsa.

Duk diramar da ake ci gaba da yi tsakanin bangarorin biyu, har zuwa yanzu babban bankin ƙasa da ya bullo da sabon tsarin sauya fasalin kuɗin bai faɗa wa 'yan Najeriya matakinsa na gaba ba.

Sakamakon haka mutane da yawa sun shiga waswasi yayin da 'yan kasuwa a sassa daban-daban na ƙasar nan suka fara daina karban tsoffin kuɗi.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: CBN Ya Zo Da Sabon Shiri Mai Kyau Na Kawo Karshen Karancin Sabbin Kuɗi a Najeriya

Shin CBN zai ƙara buga sabbin takardun naira?

A ranar Asabar da ta shige, CBN ya yi bayanin cewa ko kusa Emefiele bai alaƙanta halin matsin da al'umma suka shiga na karancin kuɗi a hannu da rashin kayan buga naira ba.

Da farko dai wani rahoto ya yi ikirarin cewa Godwin Emefiele yace sashin buga kuɗi basu da kayayyakin da zasu buga sabbin kudin a halin yanzu, lamarin da CBN ya karyata.

A wani labarin kuma Babban bankin Najeriya watau CBN na shirin raba sabbin kudi N1trn ga bankunan Kasuwanci yau Litinin

Wasu bayanai daga hanun mamban majalisar gudanarwan bankin sun nuna cewa CBN na iya bakin kokari wajen tsamo mutane daga ƙuncin karancin naira a hannu.

Jami'in ya bayyana ci gaban da aka samu da shirin da CBN ya kammala a halin yanzu wanda zai kawo ƙarshen karancin takardun naira a hannun yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel