Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

Amarya Ta Antayawa Uwarginta Tafasashen Ruwa Kan Zargin Maita A Jihar Kwara

  • Wata matar aure ta kona Uwargidanta da tafasasshen ruwa tare da lakada mata duka
  • Yan sanda sun gurfanar da ita gaban kotu da karanto kushin tuhuma guda biyu akan matar mai shekaru 42
  • Alkalin kotun ya dage sauraron karar tare da bawa yan sanda damar tsare ta a hannun su don fadada bincike kamar yadda mai gabatar da kara ya bukata

Jihar Kwara - An tsare wata matar aure mai shekaru 42, Lola Abdulsalam gidan ajiya da gyaran hali, a Illorin babban birnin Jihar Kwara, bisa zargin shekawa Uwargidanta, Bilkisu Abdulsalam ruwan zafi.

A ranar Juma'a ne yan sanda suka gabatar da Lola a gaban kotu bisa zargin laifuka guda biyu. Na farko shine zargin cin mutunci da kuma bata suna, wanda ya saba da sashe na 257 da kuma 292 na kundin penal code.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan Jihar Da PDP Ke Mulki Zai Rufe Masallatai Da Coci-Coci A Jiharsa, Ya Bada Dalili

Taswirar Kwara
Wata Amarya Ta Sheka Wa Uwargidanta Tafasasshen Ruwa A Jihar Arewa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

A bayanan yan sanda, matar da ake kara tayi zagi hadi da cin mutunci ga Bilkisu lokacin da take kokarin cire mataccen bera a bayan kofa, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

kamar yadda aka rubuta a takardar kara:

''Wadda ake karar Lola ta fara dukan Bilkisu da tsintsiya, tana ce mata mayya kafin daga bisani ta shiga kitchen ta dauko tafasasshen ruwa akan wuta ta sheka mata a jiki, inda ta barta da mummunar kuna a fuska, nono, da kuma sauran sassan jikinta.
''An garzaya da matar asibitin Cottage, da ke Olorunshogo, Illorin, inda aka kwantar da ita don magani."

Mai gabatar da kara ASP Zacheus Folorunsho, ya roki kotu da ta bar wadda ake kara a hannun yan sanda don karasa gudanar da bincike akan lamarin.

Mai shari'a Ibrahim Dasuki, wanda ya jagoranci zaman kotun, ya karbi rokon masu karar tare da dage sauraron karar zuwa 6 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matashi ya shiga hannu yayin da ya lababo zai sace janaretan kotu

Matar Aure Ta Watsa Wa Kishiyarta Ruwan Zafi A Kano

A wani rahoton mai kama da wannan, yan sandan jihar Kano sun kama wata matar aure mai suna Hauwa Auwal yar shekara 30 a unguwar Shekara Sabuwar Abuja, karamar hukumar Kumbotso kan zargin antayawa kishiyarta mai suna Sha'awanatu Mohammad ruwan zafi.

Mai magana da yawun yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa jaridar The Punch afkuwar lamarin a yayin da aka tuntube shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel