Gwamna Obaseki Ya Kori Kwamishinansa Bisa Zargin Ba Ya Tabuka Komai

Gwamna Obaseki Ya Kori Kwamishinansa Bisa Zargin Ba Ya Tabuka Komai

  • Gwamna Obaseki na jihar Edo ya bayyana korar daya daga cikin kwamishinoninsa bisa zargin baya aikin da aka saka shi
  • Gwamnan ya kuma godewa tsohon kwamishinan bisa gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Edo
  • Ana yawan samun lokutan da gwamnoni ke korar mukarrabansu saboda wasu matsaloli da suke gani

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya sanar da korar kwamishinansa na hanyoyi da gadoji, Engr Newton Okojie bisa zargin baya tabuka komai a aikinsa, Daily Trust ta ruwaito.

Obaseki ya sanar da korar kwamishinan ne a cikin wata sanarwa da kwamishinansa na sadarwa da wayar da kan jama'a, Mr Chris Osa Nehikhare ya fitar a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba a Benin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa

Obaseki ya kori kwamishinansa
Gwamna Obaseki Ya Kori Kwamishinansa Bisa Zargin Ba Ya Tabuka Komai | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sanarwar ta ce:

“Abin takaici ne yadda ba mu iya samun daman ci gaban da ayyukan hanyoyinmu ba musamman a cikin watanni 12 da suka wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kuma abin bakin cikin ma shi ne, kwamishinan duk da kokarin da ya yi, bai samar da wani gagarumin ci gaba ba ga gwamnatin jihar a kudurin cimma burinta.”

Na gode da kokarin kwamishina, inji gwamna Obaseki

Sai dai, a bangare guda gwamnan ya yaba da kokarin kwamishinan tare da yi masa godiya bisa gudunmawar da ya bayar.

A cewar sanarwar da Vanguard ta samo:

"Gwamnan ya kuma godewa kwamishinan bisa gudunmawar da ya ba jihar kuma yana mishi fatan alheri a aikinsa na gaba."

Hakazalika, ya umarni sakataren dindindin na ma'aikatar, Engr. Osikhena Omoh Ojior, da ya ci gaba da rike mukamin zuwa nan da wani lokaci.

Kara karanta wannan

Wata Fatima Abubakar Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci, Tace Ta Tsani Aure a Rayuwarta

Ana yawan samun lokuta mabambanta da gwamnoni ke sauke kwamishinoninsu saboda gaza cimma burin gwamnatin jiha.

CBN da NMfB Sun Fara Bibiyar Asusun Wadanda Suka Ci Bashin Banki Na Lokacin Korona, Suna Cire Kudi

A wani labarin, babban bankin Najeriya (CBN) da kuma bankin NIRSAL sun fara karbo kudaden da suka ba 'yan Najeriya rance a 'yan shekarun baya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an fara karbo kudaden ne a ranar Juma'a 28 ga watan Oktoban 2022 ta hanyar amfani da lambar bankin bai daya na BVN.

Hakazalika, bankin na NIRSAL zai fara dawo da kudaden da 'yan Najeriya suka karba a lokacin Korona karkashin shirin TCF da kuma na 'yan kasuwa karkashin shirin AGSMEIS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel