Turawa Sun Fi Sonmu Bakaken Fata Fiye da Larabawan da Muke So Ido Rufe

Turawa Sun Fi Sonmu Bakaken Fata Fiye da Larabawan da Muke So Ido Rufe

  • Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya ya bayyana cewa, Turawa sun fi son bakaken fata fiye da yadda Larabawa ke kaunarsu
  • Ya kuma bayyana cewa, bakaken fata na son Larabawa, amma basu fiye son bakar fata ba sai dai idan ya iya Turanci ko kwallon kafa
  • A cewarsa, Turawa suna kashe kudi kan dan Afrika saboda kauna, amma duk da haka kallon sharri ake yi masa a wannan nahiyar

Najeriya - Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, alamu masu karfi sun nuna Turawa sun fi son bakaken fata fiye da Larabawa.

Daurawa ya ce, bakaken fata Musulmai na kaunar Larabawa, amma kwata-kwata su Labarawan ba wani son bakake suke ba.

A cewarsa, Larabawa sun fi nuna sha’awa da kaunar Turawa, yayin da su kuma Turawan ke tsoro da gyamar Larabawa a cikinsu.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Malam Daurawa ya ce turawa sun fi son bakaken fata, bakake sun fi Larabawa
Turawa Sun Fi Sonmu Bakaken Fata Fiye da Larabawan da Muke So Ido Rufe | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Daurawa ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyon da aka yada a kafar Facebook, inda yake bayyana alaka tsakanin duniyar bakin fata Musulmi, Bature da Balarabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar malamin, bakin fata Musulmi na daukar Balarabe da muhimmanci, tare da yi masa kallon na kusa da addininsa kuma dan uwa, alhali Bature ya fi tausayinsa.

Turawa ne ke ba bakaken fata tallafi

Ya kuma bayyana cewa, mafi yawan kayayyakin tallafin karatu da magani da sauran abubuwa da ake ba bakaken fata sukan fito ne daga hannun Turawa.

Duk da haka, ya ce bakaken fata kallon tallafin da ya fito daga hannun bature suke a matsayin wani shiri na kawo barna a cikin al’umma.

A kalamansa, cewea ya yi:

“Mu mutanen Afrika Allah ya jarabce mu da son Larabawa amma su basu fiye sonmu da yawa ba. Kuma Allah ya jarabce mu da kin Turawa, amma kuma Turawa sun fi sonmu da son mu’amala damu da tausayinmu fiye da Larabawa a wannan zamanin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Saura kiris zabe, dan takarar gwamnan PDP a wata jiha ya kwanta dana

“To za ka ga taimakon da ke zuwa mana a Afrika kaso 65% daga kasashen Turawa ne. Amma duk da haka, ko maganin Bature ne sai kaji an ce anya, wannan mugu ne fa. Ina jin abin nan fa akwai mugunta a ciki.
“Duk abin da ya fito daga Bature ko ruwan sha ne mutum sai ya tuhume shi, ko mai kyansu kuwa. Kuma sonmu suke su yi ta kashe kudi, watakil kuma ba sonmu suke ba, cutar ce basa son ta tashi ta je wurinsu, sai su tare a nan a kashe ta.”

A cewarsa, Turawa na turo kudi a gyara ilimi, a yi hanyoyi a gyara zaizaiyawar kasa da sauran ayyukan ci gaba a Afrika.

Komai Balarabe ya ba dan Afrika alheri ne, a fahimtar mutane

A cewar Malam Daurawa, mutane suna karbar dukkan abin da ya zo daga hannun Larabawa hannu bibbiyu ko da kuwa menene saboda alaka ta addini.

Kara karanta wannan

Aljannar duniya: Daki mai kama da kanti na mata 'yar Arewa ya girgiza intanet

A bangare guda, ya ce abubuwa guda biyu ne ke sa Balarabe ya so bakin fata; iya Turanci da kuma kwallon kafa.

Ya ce abubuwan da suke fara dubawa a bakin fata ba addini ne ko wani abu ba, sun fi mai da hankali ga kwarewarsa a kwallon kafa ko kuma murda harshe a zabga Turanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.