Karancin Mai da Sauya Fasalin Naira Duk an Yi Ne Don Kawo Tsaiko Ga Zabe, Inji Tinubu

Karancin Mai da Sauya Fasalin Naira Duk an Yi Ne Don Kawo Tsaiko Ga Zabe, Inji Tinubu

  • Bola Ahmad Tinubu ya ce akwai makarkashiya game da sauyin Naira da gwamnatin Buhari ta yi a kwanakin nan
  • Hakazalika, ya ce ana kitsa kawo tsaiko ne ga zaben 2023 mai zuwa nan kusa ganin yadda ake fama da karancin mai
  • Tinubu dai shine dan takarar shugaban kasa na APC, kuma akwai alaka mai karfi tsakaninsa da gwamnatin Buhari

Jihar Ogun - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana zargin akwai wani shiri dangane da karancin man fetur a Najeriya da kuma batun sake fasalin kudi.

Tinubu ya bayyana abin da ke ransa ne a birnin Abeokuta na jihar Ogun yayin gangamin kamfen dinsa na takarar shugaban kasa, Daily Trust ta ruwaito.

A hasashen Tinubu, duk wani batu da ake kai ruwa rana dashi game da karancin man fetur da kuma sauya fasalin Naira batu ne na kawo tsaiko ga zaben shugaban kasa da ke tafe.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Karrama Babban Malamin da Aka Ƙona Kurmus a Arewa

Tinubu ya kunto kura
Karancin Mai da Sauya Fasalin Naira Duk an Yi Ne Don Kawo Tsaiko Ga Zabe, Inji Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Tinubu ya shaidawa taron jama’a cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ba sa son wannan zaben ya faru. Suna son su durkusar da shi. Za ku bar su?

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya sha alwashi tare da alkawartawa ‘yan Najeriya cewa, zai kawo karshen matsalar karancin man fetur a kasar.

Ya kuma bayyana cewa, zaben bana zai zama wani babban sauyi a Najeriya.

'Yan Najeriya za su taka da kafarsu don kada kuri'a

Da yake magana, Tinubu ya bayyana gwarin gwiwar cewa, yana da yakinin 'yan Najeriya za su taka da kafarsu don kada masa kuri'u a zabe ba tare da la'akari da abin hawa ba.

Tsohon gwamnan na Legas ya ce, zaben 2023 wani sauyi ne ga Najeriya, kuma tabbas sai an yi zaben, rahoton Premium Times.

A kalamansa:

"Sun fara zuwa da wani uzurin babu man fetur. Kada ku damu, idan ma babu mai, za mu taka don kada kuri'unmu.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda yan Najeriya suka cika bankuna don mayar da tsaffin kudi

"Idan kun ga dama, ku kara kudin farashin man, ku boye man ko kuma ku sauya launin Naira, za mu ci zaben nan."

Ana fama da karancin man fetur a kwanakin nan a Najeriya kuma gashi na ta cece-kuce game da sabbin kudi, musamman 'yan kasuwa a wasu jihohin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel