Kayan Alatun Dakin Wata Mata a Arewacin Najeriya Ya Girgiza Zaman Lafiyan Intanet

Kayan Alatun Dakin Wata Mata a Arewacin Najeriya Ya Girgiza Zaman Lafiyan Intanet

  • Wani bidiyo na ci gaba da yin kaurin suna a kafar sada zumunta na dakin wata mata da aka nuna a Najeriya
  • A bidiyon, an ga daki makare da kanta kamar na shago, inda aka jera takalma, jakunkuna, kayan sakawa da turare masu yawa
  • Wanda ya yada bidiyon ya yi ikrarin cewa, dakin wata diyar tsohon gwamnan jihar Zamfara ne a Arewa maso Yamma

Idan ana maganar kwalliya da kwalisa, mata basu ba wannan fanni kunya, kuma suka ci gaba da jawo cece-kuce a Najeriya.

A wani bidiyon da @limelittetv ya yada, an nuna cikin dakin wata mata attajira da ta tara kayan duniya masu ban mamaki.

A bidiyon, an ga kanta a cikin dakin, ga kuma tarun takalma, jakunkuna, turare da dauran kayayyakin more rayuwar duniya.

Kayan alatu a gidan wata mata ya jawo cece-kuce
Kayan Alatun Dakin Wata Mata a Arewacin Najeriya Ya Girgiza Zaman Lafiyan Intanet | Hoto: @limelittetv
Asali: Instagram

Daga gani babu tambaya, daki ne na masu hali, kuma alamu sun nuna an kashe miliyoyin kudade kafin fidda irin wannan kayan kwalisa.

Kara karanta wannan

Na Kasa Yarda: Uwa Ta Gano Abubuwan Ban Mamaki a Jakunkunan Makarantar Yaranta, Ta Saki Bidiyo

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Wanda ya yada bidiyon ya yi ikrarin cewa, dakin wata diyar tsohon gwamnan jihar Zamfara ne, amma da yawa sun karyata haka.

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:

_________sya:

“Alaye idan kina da kudi za ki yi irin wannan mana, daidai ne a wurin mata.”

symply_gifty:

“Wannan daidai ne ga mata tsaka-tsakin dakin mace ‘yar Najeriya.. babu wani abu sabo a nan.”

lovely_collection_hairs:

“Amma ai na diyar ne ba mahaifin ba, na biyu ba lallai ace da kudin mahaifin aka yi ba. Ko da mutanen da ba sa gwamnati suna da irin wadannan kayayyakin.

blestq:

“Dakata, ta ce gwamnan? Meye matsalarku? Mai yiwuwa mijinta ya fi mahaifin kudi. Ku ke kwantar da hankalinku.”

dammyola33:

“Ko da wadanda iyayensu ba ‘yan siyasa ba za su iya yin wannan ko fiye. Me yake damun mutane ne. Don kawai ‘yan bindiga sun daidaita birnin shikenan sai ‘ya’yansa su mutu. Mutane dai da irin gurbataccen tunaninsu.”

Kara karanta wannan

Ka ci digiri: Bayan zama lauya, matashiya ta kama sana'a, ta ce burinta ta zama tela

Daga siyan kunun aya, ya angwance da mai talla

A wani labarin kuma, kunji yadda wani kwastoma ya shiga daga ciki da wata mai siyar da kunun aya da zobo a kafar Twitter.

Rahoton da muka samo daga shafin matar ya nuna yadda suka fara magana da kuma yadda soyayya ta kullu.

An ce sun yi aure a farkon wannan shekaran, ta dalilin haduwa a shafin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel