Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Abia, Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne Ya Rasu

Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Abia, Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne Ya Rasu

  • A yau Laraba 25 ga watan Janairu ne dan takarar gwamnan PDP a jihar Abia ya kwanta dama bayan wata jinya
  • Dr Chikezie Uche-Ikonne, da ga dan takarar gwamnan ne ya sanar da rasuwar mahaifinsa a cikin wata sanarwa
  • Ya zuwa yanzu dai jam'iyyar PDP bata yi martani ba, ba a kuma bayyana wanda zai maye gurbin farfesa Eleazar Uchenna Ikonne ba

FCT, Abuja - Yanzu muke samun labarin cewa, dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Abia Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne ya kwanta dama.

Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwa da dansa, Dr Chikezie Uche-Ikonne ya fitar a yau Laraba 25 ga watan Janairu, New Telegraph ta ruwaito.

A tun farko, an daina ganin dan takarar na PDP a tarukan kamfen kafin samun labarin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Karrama Babban Malamin da Aka Ƙona Kurmus a Arewa

Allah ya yiwa dan takarar gwamnan PDP rasuwa
Dan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Abia, Farfesa Eleazar Uchenna Ikonne Ya Rasu | Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Sanarwar da dan nasa ya fitar kuma Daily Trust ta samo ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ina mai bakin cikin sanar da mutuwar mahaifina, farfesa Eleazar Uchenna Ikonne, wanda ya rasu a asibitin tarayya da ke Abuja a yau 25 ga watan Janairun 2023 da misalin karfe 4 na asuba bayan gajiriyar rashin lafiya.
“Ya fara samun sauki bayan samun kulawa ta musamman a Burtaniya amma ya sanke kwanciya kwanaki hudu da suka gabata wanda hakan ya kai ga bugun zuciya wanda bai samu waraka ba.
“Karin bayani da duk wasu shirye-shirye za su bayyana ga jama;a bayan tattaunawa da ganawa da ahalinsa.”

Ya rasu gabanin zabe

Marigayin dai ya rasu ne akalla wata guda da 'yan kwanaki kafin yin zaben gwamna a Najeriya.

Wannan na nufin, jam'iyyar PDP za ta sanar da wanda zai maye gurbinsa nan da zaben gwamna na 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana tsadar abinci, dakin ajiyan kamfanin abinci ya kone kurmus

Tun da farko gwamna mai ci a jihar Abia ya sanar da cewa, dan takarar da yake so ya gaje shi ya kwanta rashin lafiya, yana asibiti.

Legit.ng ta tuntubi Isah Usman, wani lauya mazaunin Zaria a jihar Kaduna don jin abin da doka ta tanada game da maye gurbin dan takarar. Ga abin da yake cewa:

"Yana da bambanci da ace gwamna ne ya rasu. Idan gwamna ne ko shugaban kasa abu ne sananne, 'deputy' mataimakinsa ne zai maye gurbinsa, hakan ya faru kan Goodluck Jonathan lokacin da 'Yar'adua ya rasu.
"A wannan yanayin, ba haka yake ba, akwai sabuwar dokar zabe da Buhari ya sanyawa hannu, ta tanadi abubuwa irin wadannan nan. Ba zan iya tunawa kai tsaye ba yanzu, amma dai za a sake zaben fidda gwani ne cikin kwanaki 14."

Dan takarar majalisa na PDP ya rasu

A wnai labarin kuma, kunji yadda dan takarar majalisar dokokin Najeriya a jihar Kebbi, Abba Bello Muhammad ya kwanta dama.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Takarar Gwamna a Arewa Ya Janye, Ya Koma Bayan Jam'iyar PDP

Wannan lamari ya faru ne a watan Janairun nan, kwanaki kadan kafin babban zaben 2023 da za a yi a Najeriya.

Shi ma Abba dai dan takara ne a jam'iyyar PDP a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel