Za a Iya Samun Matsalar Soke Zaben 2023 Saboda Rashin Tsaro, Inji INEC

Za a Iya Samun Matsalar Soke Zaben 2023 Saboda Rashin Tsaro, Inji INEC

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce akwai yiwuwar a soke zaben 2023 ko kuma a dage shi saboda matsalar tsaro
  • Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban hukumar yayin wani taron da aka gudanar game da zaben 2023
  • Ana ci gaba da fuskantar barazana a Najeriya game da zaben 2023, wasu na dasa ayar tambayar shin za a yi zaben kuwa

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi gargadin cewa, zaben bana da ke tafe nan da wata guda zai iya samun tasgaro saboda yawaitar rashin tsaro a Najeriya.

A cewar hukumar, akwai yiwuwar a samu barazanar soke zaben matukar matsalolin tsaron kasar suka ci gaba da faruwa.

Wannan batu dai na fitowa ne daga shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu yayin da ya zamu wakilcin shugaban cibiyar zabe ta BEI, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru a ranar Litinin a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Dauki Babban Alkawari a Gaban Buhari a Yola, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

INEC ta ce akwai yiwuwar a soke zaben 2023
Za a Iya Samun Matsalar Soke Zaben 2023 Saboda Rashin Tsaro, Inji INEC | Hoto: dailypost.com
Asali: UGC

Zuru ya yi gargadin ne a wani taron horarwa kan tsaron zabe da aka gudanar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za mu iyakar kokarinmu don ganin an yi zabe

A cewarsa, hukumar zabe na aikin da ya dace don tabbatar da an yi zabe lafiya kuma cin lumana, amma idan aka yi rashin sa'a matsalolon tsaro suka ci gaba da ta'azzara, hukumar za ta san na yi.

A kalamansa:

"Bugu da kari, idan ba a sanya ido kan lamarin tsaro kuma aka magance shi ba, zai kai makuran da za a soke zabe ko kuma dage shi a wasu mazabun masu yawa don gujewa matsala ga sakamakon zabe da kuma rikicin kundin tsarin mulki da ka iya faruwa baktatan.
"Ba za a bari wannan ya faru ba kuma bai ma kamata a bari ya faru ba."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'ai Sun Ceto Mutum 6 Cikin Wadanda Miyagu Suka yi Garkuwa Dasu a Filin Jirgin Kasan Edo

Abin da hukumomin tsaro ke cewa, INEC ta magantu

A bagare guda, Zuru ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa hukumomin tsaro kama da kan mai ba shugaban kasa shawari har shugabannin hafsoshin tsaro sun ba 'yan Najeriya tabbacin za a yi zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Hakazalika, ya ce hukumar ta zaben zaben na yin duk mai yiwa don tabbatar da an yi zaben kana an fitar da sakamako daidai da yadda sabon kundin zabe na 2021 ya tanada.

Tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida kuwa ya bar kasar nan, don gujewa matsalar da ka iya biyowa a lokacin babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel