Tsohon Shugaban Kasa, IBB Ya Tafi Kasar Jamus, Zai Dawo Bayan Zaben 2023

Tsohon Shugaban Kasa, IBB Ya Tafi Kasar Jamus, Zai Dawo Bayan Zaben 2023

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shilla kasar waje yayin da ake shirin babban zaben 2023 na bana
  • IBB ya shilla kasar Jamus ne don gujewa cece-kuce da kuma abin da ka iya biyo bayan babban zaben 2023 da ke tafe nan kusa
  • Ba wannan ne karon farko da tsohon shugaban kasa ke daukar matakin barin kasa ba a daidai zaben shugaban kasa

Najeriya - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Janar Ibrahim Babangida IBB ya shilla kasar Jamus kamar yadda rahotanni daga jihar Neja suka tabbatar, Leadership ta ruwaito.

An gano cewa, IBB ya yi tafiya ne a ranar Asabar tare da dansa, Aminu da kuma wani hadiminsa daya, kuma zai dawo Najeriya ne bayan kammala zaben 2023.

An tattaro cewa, ya tashi ne a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda ahalinsa suka taru don yi masa bankwana.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

IBB ya tafi kasar waje
Tsohon Shugaban Kasa, IBB Ya Tafi Kasar Jamus, Zai Dawo Bayan Zaben 2023 | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Dalilin tafiyar IBB zuwa kasar Jamus

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani dangin kusa ya shaida cewa, IBB ya yi wannan tafiyar ne kamar yadda ya saba don kaucewa cece-kuce daga 'yan siyasa gabanin zabe, kana don ya duba lafiyarsa a can.

A cewar majiyar ta shaidawa Leadership cewa:

“Babu shakka mai girma tsohon shugaban kasa bai son a ambace shi ko a ta’allaka shi da wani cece-kuce da ka iya tasowa a lokacin zabe don haka ya yanke shawarin yin tafiya.
“Tuntuni ma wasu ‘yan takarar shugaban kasa na neman ganawa dashi a fili amma ya ki don haka ya yanke shawarin barin kasar a madadin haka.”

Wata majiyar kuma ta bayyana cewa, a watannin Nuwamba da Disamban bara, IBB ya gana wa gwamnonin jihohi don yin sharar fage ga dan takarar shugaban kasa da yake so, amma ya watsar da hakan kamar yadda ya saba.

Kara karanta wannan

2023: El-Zakzaky na marawa Peter Obi baya? Gaskiya ta fito, ya fadi matsayarsa

Ba wannan ne karon farko ba

An tattaro cewa, IBB zai zauna a kasar Jamus na tsawon watanni uku, kuma zai dawo Najeriya ne ana gab da fara azumin watan Ramadana.

Idan za ku iya tunawa, a lokutan zaben 2015 da 2019, IBB ya yi tafiyar watanni gabanin babban zabe, inda ya dawo gida Najeriya bayan makwanni da yin zaben.

A kan zargi tsoffin shugabannin Najeriya da yin tasiri matuka a lokutan zabe a kasar, don haka IBB yake gujewa cece-kuce.

A baya an yada jita-jita cewa, IBB ya marawa Peter Obi baya, amma wata sanarwa daga hadiminsa ta karyata rahoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel