Zamu Fatattaki Yunwa da Jam'iyyar Mayunwata a 2023, Bola Tinubu

Zamu Fatattaki Yunwa da Jam'iyyar Mayunwata a 2023, Bola Tinubu

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC mai mulki ya yi alkawarin magance yunwa da talauci idan ya ci zabe
  • A wurin gangamin kamfen APC wanda aka shirya a Yola, Bola Tinubu ya rada wa jam'iyyar adawa PDP wani suna
  • Shugaban kasa Buhari ya roki mazauna Adamawa su taimaka su sake amincewa APC a zaben watan Fabrairu

Adanawa - Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tiɓubu, ranar Litinin yace gwamnatinsa zata kawar da yunwa idan aka zabe shi a 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Tinubu ya dauki wannan alkawarin ne a Yola yayin da jirgin yakin neman zabensa ya dira jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Gangamin APC a Adamawa.
Zamu Fatattaki Yunwa da Jam'iyyar Mayunwata a 2023, Bola Tinubu Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

A jawabinsa, Bola Tinubu ya ce:

"Duk abinda suka yi a jam'iyyar ci gaban Talauci, kun san sunan su jam'iyyar raya Talauci (Poverty Development Party, PDP) zamu sauya maku shi zuwa farin ciki, kwanciyar hankali, jin dadi da samun aiki."

Kara karanta wannan

Adamawa Ta Cika Ta Batse Yayin da Shugaba Buhari Ya isa Mahaifar Atiku Don Yakin Neman Zaben APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan jihar Legas din ya kara da cewa gwamnatinsa zata mai hankali kacokan kan al'umma, inda ya ce, "Ku tsammaci cewa zamu jawo ku yadda ya kamata."

"Zamu ɗauke ku aiki kuma zamu saurari dukkan bukatun ku."

Ku zabi Tinubu ya gaje ni - Buhari

A nasa jawabin, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roku mutanen Adamawa su zabi dan takarar APC, Asiwaju Bola Tinubu, domin goben Najeriya ta yi kyau, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A gangamin yakin neman zaben APC da ya gudana a Yola.yau Litinin, Buhari ya kuma bukaci mazauna Adamawa su kada wa Sanata Aishatu Binani kuri'unsu ta zama gwamna ta farko mace.

"Na zo gare ku yau ina rokon ku jefa wa 'yan takarar jam'iyyar APC kuri'unku. Bola Tinubu zai yi aiki ba gajiyawa domin kasar nan kuma ku zabi Aisha Binani a matsayin gwamna mace ta farko a Adamawa."

Kara karanta wannan

Shin Gwamnonin APC 11 Na Tare da Atiku? Gwamnan Arewa Ya Magantu, Ya Fadi Abu 1 Da Zai Iya Hana Tinubu Cin Zabe

"Ku mutanen Adamawa zaku iya kafa tarihi idan kuka zabi gwamna mace ta farko kuma ku sani muna alfahari da ku."

- Muhammadu Buhari.

A wani labarin kuma Mun tattara maku abinda shugaba Buhari ya gaya wa al'ummar Adamawa game da zaben mace fa shugabance su

Shugaban kasa Buhari ya ce mata sun cancanci su jagoranci al'umma, ya nemi mutanen Adamawa su zabi Aishatu Ahmed Binani a 2023. Shugaban yace zai ci gaba da baiwa Sanata Binani dukkan goyon bayan da ta bukata da sauran yan takarar APC domin su doke abokan hamayya a zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel