Abin da INEC Take Tsoro Ya Auku, An Sake Kai Wa Ofishin Hukumar Zabe Hari

Abin da INEC Take Tsoro Ya Auku, An Sake Kai Wa Ofishin Hukumar Zabe Hari

  • A wani jawabi, INEC ta ce an sake kai mata hari a ofishinta da ke karamar hukumar Isu a Jihar Imo
  • Hukumar gudanar da zabe ta bada wannan sanarwa ne ta bakin Kwamishinan labarai, Festus Okoye
  • Okoye ya ce jami’in REC na Imo ya sanar da hukumar game da harin da aka sake kai wa INEC a Imo

Imo - Hukumar gudanar da zabe na kasa watau INEC, ta ce an kai wa ofishinta da ke karamar hukumar Isu a jihar Imo wani hari a makon nan.

The Nation ta ce Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar INEC, Festus Okoye ya fitar da jawabi a game da lamarin a jiya.

Da yake bayani a garin Abuja, Festus Okoye ya ce Kwamishinan zabe na jihar Imo, Farfesa Sylvia Uchenna Agu ya sanar da INEC a game da harin.

Hukumar ta ce abin takaicin ya faru ne da safiyar ranar Talata, 20 ga watan Disamba 2022. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a yammacin Laraba.

Bayanin harin da aka kai

"An ruguza tagogi takwas, sannan an cire wasu shingogi. Sai dai an yi dace maharani ba za su iya shiga cikin ginin ofishin hukumar ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba a dauke ko lalata wasu kaya da za a iya tafiya da su ko wadanda suke ajiye a wuri daya ba.

- Festus Okoye

Jami'in tsaro a Najeriya
Jami'in tsaron NSCDC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC
Domin ayi rigakafi, an dauke muhimman kaya irinsu akwatuna da rumfofin kada kuri’a daga ofishin, an boye su a wani ofishin INEC.
Baya ga haka, an adana duk wasu katin PVC da ba a karba ba, kuma za a kai jami’an tsaro domin ganin mutane sun karbi katinsu."

- Festus Okoye

Jami'an tsaro sun samu labari

Rahoton ya ce an sanar da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin a dauki matakin da ya dace, ganin wannan ne hari na hudu da aka kai a Imo.

A cikin kusan makonni uku, tsageru sun aukawa ofisoshin hukumar INEC a kananan hukumomin Orku da Oru, sannan an je har hedikwatar jihar a Owerri.

A rahoton da gidan talabijin na Channels TV ta fitar, an ji cewa jami’an tsaron NSCDC sun ja kunnen mutane a game da wadannan danyen aiki da ake yi.

Abin da muke tsoro - INEC

Kwanan nan aka rahoto Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce a shekaru uku da rabi, ‘yan ta’adda sun kai wa INEC hari har sau 50 a jihohi 15.

Mahmood Yakubu ya ce muddin aka kai shekara mai zuwa ba a daina kai wa hukumar INEC hari ba, za a iya samun matsala wajen shirya zabuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel