Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Rufe Titin Gusau-Dansadau, ‘Yan Sa Kai Sun Sheke 15

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Rufe Titin Gusau-Dansadau, ‘Yan Sa Kai Sun Sheke 15

  • Miyagun ‘yan bindiga a ranar Asabar sun kai harin daukar fansa kan matafiya a babban titin Gusau zuwa Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara
  • An gano cewa, ‘yan bindigan sun fara kai hari kauyen Maigoge inda suka yi artabu da ‘yan sa kai har suka halaka ‘yan bindiga 15 a take yayin da sauran suka tsere
  • Dole ta sa jami’an tsaro suka kai wa matafiya daukin gaggawa inda suka dinga yi musu rakiya cikin tawaga, lamari da yasa miyagun suka arce

Zamfara - Tsagerun ‘yan bindiga a ranar Asabar sun rufe babban titin Gusau zuwa Dasadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, Daily Trust ta rahoto.

‘Yan bindiga
Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Rufe Titin Gusau-Dansadau, ‘Yan Sa Kai Sun Sheke 15. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

‘Yan bindigan sun dinga kai farmaki kan masu ababen hawa da matafiya a kan titin mai tsawon kilomita 100. An tattaro cewa ’yan ta’addan sun dinga kaiwa gomman matafiya kan hanyar.

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: 'Yan sanda sun kama wasu tsagerun masu garkuwa da mutane

Na tsawon lokaci, jami’an tsaro suka dinga raka matafiya har zuwa garin Dansadau don gujewa farmaki. Matafiyan sun dinga raka jama’a a tawaga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Dansadau ya sanar da Daily Trust cewa ‘yan bindigan sun rufe titin da niyyar garkuwa da mutane tare da halaka matafiya amma tawagar sojoji suka fatattakesu da gaggawa.

Dansadau yace:

“Sun tsara kansu a wurare masu hatsari da ake kira Mashayar Zaki. Wurin ya kasance inda masu ababen hawa ke tsoro.
“Yanzu an gyara titin kuma matafiya na tafiya lafiya kalau duk da suna kiyayewa. Tun farko ‘yan bindigan sun kai farmaki Maigoge, wani yanki mai nisan kilomita 8 yammacin Dansadau amma suka yi artabu da ‘yan sa kai. ‘Yan sa kan sun halaka 15 daga cikinsu.
“Da safen nan, ‘yan bindigan sun dawo domin daukar fansa a yankin. Sun zo da yawansu kuma a babura. Jirgin yaki ya isa babu dadewa.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Sheke Tsohuwa Mai Shekaru 120 tare da Wasu 5

“Jirgin yakin ya zagaya Dansadau sannan ya karasa kauyen Maigoge. Sai dai bamu da tabbacin me ya faru bayan zuwan jirgin.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, bai riga da yayi tsokaci kan lamarin ba.

Yan Sanda sun kama ‘yan bindiga 7, sun ceto mutum 15

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da damke ‘yan bindiga 7 bayan samamen da jami’an suka kai maboyarsu.

Sun yi nasarar ceto mutum 15 da miyagun suka yi garkuwa dasu a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel