Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Ta’adda 7, Sun Ceto Mutum 15

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Ta’adda 7, Sun Ceto Mutum 15

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tayi ram da wasu ‘yan bindiga bakwai bayan ta kai samame har maboyarsu a jihar Zamfara
  • Baya ga hak, ‘yan sandan sun yi nasarar ceto wasu mutum bakwai daga sansanin ‘yan bindigan da suka yi garkuwa dasu don karbar kudin fansa
  • Jami’an ’yan sandan sun kama wata mata mai safarar makamai ga ‘yan bindiga wacce ta kware a harkar amma dubunta ta cika a makon nan

Zamfara - Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta damke wasu ‘yan ta’adda bakwai tare da ceto wasu mutum 15 da aka yi garkuwa dasu.

‘Yan ta’addan Zamfara
Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Ta’adda 7, Sun Ceto Mutum 15. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wadanda aka ceto din sun kwashe kwanaki 50 a hannun ‘yan ta’addan kuma an ceto su a ranar Litinin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Yusuf Koli, yayin bayyana wadanda ake zargin a gaban manema labarai a Gusau a yammacin Alhamis, yace rundunar ba zata sassauta ba wurin kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun kama wasu kudade N19.5 a hannun abokan 'yan bindiga 5 a Arewa

A wata takarda da Premium Times ta samu, mai magana da yawun rundunar, Mohammed Shehu, yace mutum shida da ake zargi ne aka kama kan hada kai wurin laifi, tsoratarwa da tsatse kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“An samu kudi har N700,000 daga wurinsu. Kudaden suna daga cikin harajin da suka kallafawa wasu kauyukan kananan hukumomin Anka.”

- Shehu yace.

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa, Shehu yace an kama wata mata mai samarwa da ‘yan bindigan makamai wadanda suka addabi jihar.

“Wacce ake zargin ta shahara wurin safarar makamai zuwa kungiyar gagararren ‘dan bindiga Dawa.
“‘Dan bindigan mai suna Dawa ya kasance shugaban shahararriyar kungiyar garkuwa da mutane da suka kware wurin satar mutane a Zamfara da jihohin masu makwabtaka. Wacce ake zargin ta amsa laifinta kuma ana cigaba da bincike.”

- Yace.

Kara karanta wannan

Nwankwo ya Shiga Hannun ‘Yan Sanda Bayan Shekaru 7 Ana Bibiyarsa Kan Zargin Garkuwa da Mutane

Sanadiyyar ceto su

Shehu yace an ceto wadanda aka yi garkuwa dasu ne sakamakon bayanan sirri da runduna ta musamman ta ‘yan sandan ta samu.

“Rundunar ‘yan sandan tare da hadin guiwar ‘yan sa kai sun yi amfani da bayanan sirri dangane da garkuwa da mutum 15 da ‘yan ta’adda suka yi a kauyen Dike dake karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.”

Shehu yace wadanda aka ceto din an mika su asibiti domin a duba lafiyarsu kuma jami’an ‘yan sanda su yi musu bayani kafin a mika su ga iyalansu.

Yan Sanda sun ceto wadanda aka yi garkuwa dasu a Kaduna

A wani labari na daban, ‘yan sanda sun yi nasarar ceto wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa dasu a jihar Kadun.

Cike da kwarewa, ‘yan sanda sun bibiyi hanyar Barde zuwa Keffi a karamar hukumar Kafanchan ta jihar Kaduna inda suka ceto mutane bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel