'Yan Sanda Sun Kama ’Yan Bindigan da Ake Zargin Masu Garkuwa da da Mutane Ne

'Yan Sanda Sun Kama ’Yan Bindigan da Ake Zargin Masu Garkuwa da da Mutane Ne

  • 'Yan sanda sun yi nasarar kame wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane a wani yankin jihar Edo
  • An kama su ne bayan kai ruwa rana da aka yi dasu, 'yan banga sun taimaka matuka wajen kamo tsagerun
  • Ana ci gaba da samun hare-haren 'yan bindiga a Najeriya, jami'an tsaro na ci gaba da fatattakar tsageru da masu tada hankalin jama'a

Jihar Edo – Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta yi nasarar cafke wasu ‘yan bindiga mutum biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, rahoton Daily Trust.

Wadanda aka cafken sun hada da Christopher Aiyegbeni mai shekaru 29; Matthew Osayande mai shekaru 32; Uyi Destiny mai shekaru 27; Bankole Faz mai shekaru 35; da Ayemen Okojie mai shekaru 32.

‘Yan sanda daga ofishin yanki na Ekiadolor ne suka kama wadannan tsageru a ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Yaran da ake Kiyawa Ta’addanci 41,000 ne Suka Mika Wuya ga Soji, Kwamandan OPHK

An kama 'yan bindiga a jihar Edo
'Yan Sanda Sun Kama ’Yan Bindigan da Ake Zargin Masu Garkuwa da da Mutane Ne | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda aka kama ‘yan ta’addan

Mai magana da yawun ‘yan sanda, Chidi Nwanbuzor ya bayyana cewa, an kama tsagerun ne bayan samun bayanan sirri na yadda suka yi barna a sansannin Ogoja da ake fi sani da Ford Camp da ke Kamafua.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nwanbuzor ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari tare da yin harbin kai mai uwa da wabi, amma aka kama su bayan da aka hada kai da ‘yan bangan yankin.

Ya kuma bayyana cewa, an kwato bindigogi a hannun ‘yan ta’adda da kuma sauran kayayyakin aikata laifuka.

‘Yan sanda sun yaba wa jama’a

A cewarsa, kwamishian ‘yan sandan jihar, CP Mohammed A. Dankwara ya yabawa jami’an ‘yan sanda, mazauna da ‘yan banga bisa kokarin da suka yi na aikin gaggawa da kamo ‘yan ta’addan.

Hakazalika, ya bukaci jama’a da suka kasance masu hada kai da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wajen musayar bayanai don kamo ‘yan ta’addan da ke addabar jama’a, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Daga Karshe Yan Sanda Sun Magantu Kan Gano Rubabbun Kudaden Da Aka Birne

'Yan sanda da sauran jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda, musamman a kwanakin nan.

A kwanakin baya 'yan sanda suka kame wasu tsagerun da suka addabi mazauna a jihar Zamfara, an fara gudanar bincike a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel