Tinubu Ya Jawo Cece-Kucen ‘Yan Najeriya a Wani Bidiyo, Ya Ce Ana Hada ’Hand Sanitizer’ da Masara

Tinubu Ya Jawo Cece-Kucen ‘Yan Najeriya a Wani Bidiyo, Ya Ce Ana Hada ’Hand Sanitizer’ da Masara

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu na ci gaba da sa 'yan Najeriya magana tun bayan fitowarsa takarar 2023
  • A wani bidiyon da ya yadu a kafar sanda zumunta, an ji Tinubu na fadin wata magana a wani taro, inda ya yi magana kan rage zaman banza
  • Jigon APC na kusa da Tinubu, Joe Igbokwe ya ce Tinubu ya yi magana ne kan 'Agbadonomics', inda ya yi karin haske game da habakar tattalin arziki ta hanyar noman masara

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya fadi kadan daga hanyoyin da za a bi wajen kawar da zaman banza a Najeriya.

A wani bidiyon da wani jigon APC mazaunin Legas, Joe Igbowe ya yada Facebook, Tinubu ya yi magana kan wata kalma 'AGBADOnomics'

Kara karanta wannan

An Nemi Bola Tinubu An Rasa Ana Tsakiyar Kamfe, APC Ta fito Tayi Karin Haske

A cikin bidiyon, Tinubu ya bayyana meye ma'anar wannan kalmar ta 'Agbabonomic', inda ya bayyana dalla-dalla yadda 'yan kasar waje ke amfani da masara wajen yin abubuwa da yawa.

Tinubu ya jawo cece-kuce a shafin sada zumunta
Tinubu Ya Jawo Cece-Kucen ‘Yan Najeriya a Wani Bidiyo, Ya Ce Ana Hada ’Hand Sanitizer’ da Masara | Hoto: dailypost.com
Asali: UGC

A bidiyon, Tinubu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban san me suke kiran masara ba sai da na zo Amurka. Kuma daga masararmu ne.
"Wannan abun da muke amfani da shi saboda cutar Korona, ban san daga masara ake yinsa ba, masarar da muke nomawa a nan.
"Haba, wane irin adadi za mu iya nomawa? Za mu iya mamaye yankin Afrika ta Yamma. Ya kamata mu yi shi a gida. Ya kamata mu yi abubuwa da yawa a gida. Za mu samar da ayyuka."

Kalli bidiyon

Martanin 'yan Najeriya

Bayan yada wannan bidiyo, mutane da yawa sun shiga mamakin irin maganar da Tinubu ya yi, ga kadan daga abinda suke cewa:

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC Mai Ƙarfin Faɗa A Ji Ya Bayyana Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Da Ke Tayar Wa Tinubu Hankali

@aniolabdulai:

"Tabbas za mu iya yinsa a gida."
"Don Allah mu ba shi wannan daman ta rayuwa mu gani Insha Allahu."."

@abang_thankgod:

"Komai yana da nasa tushe to kenan Najeriya ke da masara, adadi nawa muke nomawa."

@lord_Emz yace:

"Jikinsa rawa yake amma mutane ba sa gani?"

@sammyniran2008 ya yi martani da cewa:

"Mun gani. Sakon da yake fadi ya fi muhimmanci a gare mu."

@Akanni1312:

"Ikon Allah!."

@bakarbelle:

"Ya san me yake magana akai...tunani mai kyau da zurfi."

An nada Tinubu sarauta a Kaduna

A wani labarin kuma, kunji cewa, dan takarar shugaban kasa na APC ya samu sarauta a Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Tinubu ya samu sarautar Dakaren Birnin Gwari ne yayin da ya kai ziyara jihar Kaduna don kaddamar da kamfen dinsa a Arewa maso Yamma.

Tinubu ya samu rakiyar jiga-jigan APC wajen nadin wannan sarauta mai matukar girma a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel