Matar Aure Ta Gano Mijinta Na Da Wata Matar Daban, Ta Dira Gidan a Wani Bidiyo

Matar Aure Ta Gano Mijinta Na Da Wata Matar Daban, Ta Dira Gidan a Wani Bidiyo

  • Bayan shekaru 25 da aurensu, wata mata ta gano sahibinta ya ƙara aure a sirrance kuma har amaryar ta haihu
  • Matar wacce zuciyarta ta karye ta yi ta maza ta kai ziyara gidan Amaryar mijin tare da ɗanta don jin ba'asi
  • Anan ne ta gano cewa ita kanta Amaryar ta shafe shekaru 10 tare da shi amma bata san yana da uwar gida ba

Bayan shekaru 25 da Aurensu, wata mata ta gano cewa abokin rayuwarta ya yi wani sabon aure a can waje ba tare da ta sani ba.

Babu cikakken bayani kan hanyar da ta bi ta bankado wannan sirri, amma matar sai da binciko har wurin da abokiyar zamanta ke zaune kuma ta kai mata ziyara ba zato.

Asirin Miji ya tonu.
Matar Aure Ta Gano Mijinta Na Da Wata Matar Daban, Ta Dira Gidan a Wani Bidiyo Hoto: @arianaxinxin
Asali: UGC

Wasu Bidiyoyi da aka wallafa a shafin TikTok. yayin da uwar gidan ta kai ziyara, ta tambayi matar cewa tana neman mijinta mai suna Donovan.

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Ɓoyayyar matar ta biyu cikin hanzari ta katse ta da cewa sunan da ta kira fa na Mijinta ne kuma shekara 10 kenan suna murza soyayyar aurensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma nuna wa uwar gidan ɗiyar da suka haifa yar shekara 9. Nan take matarsa ta farko ta shaida wa Amaryar cewa ita ma shekara 25 kenan da auren Donovan ta nuna mata karamin ɗansu.

Matan biyu dai sun yi kokarin gano musabbanin buga wannan wasan na Mijinsu yayin da Matar farko ta kokarta kiran Donovan ya kawo kansa.

Duba Bidiyon anan

Martanin mutane kan lamarin

Ahmed Mohammed yace:

"Zata iya yuwuwa matar shekara 25 ba ta san komai ba amma dole ta biyu mai shekara 10 da auren ta san abinda ke wakana."

Tawana Johnson-John yace:

"Yadda take kallon matar sai na ji kamar ta san wani abu kan lamarin amma tana kokarin buga wasan."

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Biya Kudin Jirgi Daga 'Kasar Waje Dan Ganin Saurayinta

Monika AKA tace:

"Idan har ta aure shi shekara 25 da suka shige kuma har ya iya zuwa ya ƙara aure ba tare da sakinta ba, lallai akwai rigima babba."

Wata Budurwa Ta Nemi Dan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Girgiza Mutane

A wani labarin kuma Wata dirarriyar Budurwa ta nemi wani Ɗan Acaba ya zo su kwanta su rage wa juna zafi amma martanin mutumin ya bata mamaki

A wnai gajeren bidiyo da aka wallafa a Soshiyal Midiya, budurwar ta tunkari ɗan Acaba yayin da yake jiran Allah ya kawo masa fasinja ya samu halal, ta bashi sako.

Da ya bude takardar ya karanta bukatar matar wacce ta zayyana a bayyane cewa ta amince ya zo su kwanta, sai dai mutumin ba nan ne tunaninsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel