Wata Budurwa Ta Nemi Dan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Girgiza Mutane

Wata Budurwa Ta Nemi Dan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Girgiza Mutane

  • Wani Dan Acaba ya sha yabo lodi-lodi a soshiyal midiya bayan ya nuna akwai mutane natsattsu masu hankali har yau
  • Wata dirarriyar budurwa mai wasan barkwanci ta je wurin ɗan acaban ta bashi takarda, ta rubuta ya biyo ta idan yana son su kwanta tare
  • Yayin da ta tsaya taga matakin da zai ɗauka, Ɗan Acaban ya yaga takardar bayan fahimtar manufarta, ya ki amincewa

Wata budurwa 'yar Najeriya ta amince da cewa ba kowane namiji ne ke faɗawa tarkon yan iska ba bayan wasan barkwancin neman saduwa da wani Ɗan Acaba bai yi nasara ba.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin TikTok, yayin da budurwan ta hangi Ɗan Acaban, ta tattaka zuwa gabansa, ta miƙa masa wata yar takarda ɗauke da sako.

Wasan barkwanci.
Wata Budurwa Ta Nemi Dan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Girgiza Mutane Hoto: @omapearl
Asali: UGC

"Zamu iya jin daɗin junanmu, ka biyo ni," abinda ke cikin takardar kenan.

Kara karanta wannan

Ba Girman Kai: Zankadeɗiyar Budurwa Mai Digiri Ta Bude Wurin Wankin Mota, Bidiyonta Ya Ƙayatar da Mutane

Bayan Ɗan Acaban ya gama karanta abinda takardar ta ƙunsa, nan take ya yagata kana ya maida hankali wajen kasuwancinsa, abinda ya baiwa matashiyar mamaki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta tsaya can daga gefe tana jiran ganin matakin da zai ɗauka amma sai abun ya ba ta mamaki.

Jama'a sun yi tsokaci a Soshiyal midiya

Bedi ya ce:

"Yan uwanka maza na matukar alfahari da kai, ba mu yi arha kamar haka ba."

James D'Lowkey yace:

"Kai nifa ina ganin mutumin bai san yadda zai karanta sakon ba. Bai san abinda aka rubuta ba a ciki."

Babahaja Tsaragi yace:

"Mutumin ya gane komai dake cikin takardar, amma ya kauda kansa."

Cruz ya ce:

"Ya fahimci komai yadda ya kamata amma fa neman abinci ya fi masa amfani. Yanzu fa maza sun bazama neman kudi."

Kara karanta wannan

"Ana Cuta Na" Wani Mutumi Ya Koka Kan Yadda Ɗansa Ya Hana Shi Kwanciya da Matarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali

Starph yace:

"Suna tunanin muna bin komai muka gani a cikin zani, Gaskiya ka sa mu Alfahari."

Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Lambar Wani Mutumi a Gaban Matarsa, Bidiyon Abinda Ya Faru Ya Ja Hankali

A wani labarin, Wata matar aure ya ga karfin hali wurin budurwa yayin ta zo har gaban mijinta ta nemi lambar wayarsa lokacin suna tare

A wani bidiyon wasa, budurwa ta ga matashin kuma ta kyasa hakan ya sa ta je tana neman lambarsa a gaban matarsa, lamarin da ya kaɗa hanjin matar.

Sai dai Magidanci ya bukaci matarsa ta bayar da lambarsa ga budurwar lamarin da ya sanya ta ƙara haɗe rai ta murtuke fuska.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel