Da Dumi Dumi: DSS Ta Ba NNPC Da Dilallan Mai Awanni 48 Su Magance Matsalar Fetur

Da Dumi Dumi: DSS Ta Ba NNPC Da Dilallan Mai Awanni 48 Su Magance Matsalar Fetur

  • Hukumar DSS ta yi gargadi ga dillalan mai da sauran masu ruwa da tsaki da ke harkar
  • Rundunar tsaron farin kaya ta ce za ta fara farautar dukkanin wadanda ke da hannu a rikixin man fetur da ke gudana a yanzu a fadin kasar
  • DSS ta ce ta ba masu ruwa da tsaki a bangaren awanni 48 su kawo karshen wahalar man fetur a Najeriya

Abuja - Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta baiwa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) da kungiyar dillalan man fetur na Najeriya (IPMAN) da sauran masu ruwa da tsaki a harkar mai sa'o'i 48 su magance rikicin man fetur da ke gudana.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar DSS ta bayar da wa'adin ne a yau Alhamis, 8 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Wahalar man fetur
Da Dumi Dumi: DSS Ta Ba NNPC Da Dilallan Mai Awanni 48 Su Magance Matsalar Fetur Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Za mu kame duk wanda aka samu da hannu a wahalar man fetur, DSS

Rundunar yan sandan sirrin ta yi barazanar cewa za ta kame duk masu hannu a lamarin idan aka ci gaba da samun dogon layi a gidajen mai a kasar bayan awanni 48.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ta DSS, Peter Afunanya, ne ya bayyana hakan a hedkwatar rundunar da ke Abuja jim kadan bayan Darakta Janar na DSS ya gana da masu ruwa da tsaki.

Masu ruwa da tsakin da suka halarci taron sun hada da MOMAN, DEPMAN, IPMAN, NNPC, NARTO, NUPENG da PTD.

Yadda mutane suka dauki lamarin

Legit.ng ta tuntubi wasu mazauna garin Minna inda suka nuna goyon bayansu ga wannan mataki da DSS ta dauka domin a cewarsu da gangan wasu gidajen man ke kin siyarwa masu ababen hawa sai dai yan bunburutu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Wani mutum mai suna mallam Ibrahim ya ce:

"Zai fi kyau jami'an tsaro su zamo masu sanya idanu kan ayyukan gidajen mai. Sai ka ga mutum ya tsaya layi tun safe amma kafin a zo kansa sai ace mai ya kare kuma fa ba karewar yayi ba. A'a an dai boye sauran ne don a zo a siyarwa yan bunburutu saboda suna bayar da cin hanci.
"Su kuma yan bunburutun sai konawa jama'a hannu suke yi. A yau dinnan na siya mai kan 370 lita daya a hannun wani dan bunburutu wai ya ma mun sauki kenan. Dan Allah gwamnati da jami'an tsaro su shigo lamarin."

A nashi bangaren, mallam Abukar ya ce lallai daukar wannan mataki zai taimaka ba kadan ba domin sam hatta motocin haya sun yi wuya sosai yana mai cewa:

"Nan na je Lambata zan dawo Minna wallahi na shafe sama da awanni babu motoci a gareji, ga dai matafiya baje ta ko'ina amma babu abun hawa saboda wahalar mai."

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: 'Yan sanda sun ceto wasu mutum uku da aka sace jiya da dare a Abuja

Gwamnatin tarayya ta magantu game da karin farashin man fetur

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa za a kara farashin man fetur zuwa naira 400.

Hukumar da ke kula da man fetur ta NMDPRA ta jaddada cewar farashi na nan a yadda yake kuma ba zai sauya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel